Merkel ta yi alƙawarin taimaka wa Turkiya a kan rikicin Siriya | Labarai | DW | 31.10.2012
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Merkel ta yi alƙawarin taimaka wa Turkiya a kan rikicin Siriya

Kasar Turkiya dake zama memba a cikin ƙungiyar NATO ta ba da mafaka ga dubun dubatan 'yan gudun hijira dake ƙaurace wa yaƙin Siriya.

A dangane da taɓarɓarewar rikicin ƙasar Siriya, shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta yi wa ƙasar Turkiya alƙawarin ba ta taimako. Bayan ganawarta da firaministan Turkiya Recep Tayyip Erdogan a birnin Berlin, Merkel ta ce za a taimaka wa Turkiya dake zama memba a cikin ƙungiyar ƙawancen tsaron NATO idan buƙatar yin haka ta taso. Ta yaba da halin dattako da Turkiya ta nuna a kan rikicin na Siriya.

"Daga ɓangaren Jamus, idan an nema, mun yi tayin ba da taimakon jin ƙai, kuma a ɗaya hannun muna godiya cewa Turkiya ta nuna halin sanin ya kamata gami da ƙoƙarin ganin an kawo ƙarshen wannan rikici."

Shi dai Erdogan ya je Berlin ne don ƙaddamar da sabon ofishin jakadancin Turkiya a Jamus. A saboda muhimiyar rawar da take takawa a yankin, Turkiya na neman cikakken wakilci a cikin ƙungiyar tarayyar Turai.

Mawallafi: Mohammad Nasiru Awal
Edita: Zainab Mohammed Abubakar