Merkel ta taya Buhari murnar lashe zabe | Labarai | DW | 02.04.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Merkel ta taya Buhari murnar lashe zabe

Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta bi sahun takwarorinta shugabannin kasashen duniya wajen taya Janar Muhammadu Buhari murnar lashe zaben shugaban kasa a Najeriya.

A cikin wani sakon wayar tangaraho da Merkel ta aike wa Buhari da safiyar wannan Alhamis ta taya shi murnar samun wannan nasara. Ta ce da wannan nasara, al'ummar Najeriya sun aike da wani sako bayyanan ne na kafuwar tsarin demokaradiyya a kasarsu. Ta yi kira gare shi da ya hada karfi da karfe da sauran jam'iyyun siyasa don karfafa demokaradiyya da kuma ciyar da tattalin arzikin kasar gaba. Ta yi fatan cewa huldar danganta da hadin kai za su ci gaba da karfafa tsakanin kasashen biyu. Merkel ta yi amfani da wannan dama inda ta mika goron gayyata ga Buhari da ya kawo ziyara Jamus. Ta yi masa fatan alheri.