Merkel ta samu tabbacin kafa gwamnati | Labarai | DW | 12.01.2018
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Merkel ta samu tabbacin kafa gwamnati

Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta bayyana cewar tana da tabbacin kafa gwamnatin hadaka da jam'iyyar SPD bayan wani dogon zaman sharar fage da suka yi kan fara tattunawa kan yadda za su kafa gwamnati tare.

Shugaban jam'iyyar SPD  Martin Schulz  ya shaida wa manema labarai a daren Alhamis zuwa Juma'a cewar jam'iyyar CDU ta Angela Merkel ta amince kan a yi hadakar ne bisa sharadin wasu manufofi da za su taimaka wa kasar. An yi zaben na Jamus tun sama da watanni uku da suka gabata. Sai dai har yanzu ba a kai ga kafa gwamnati ba saboda gaza cimma matsaya daga wasu jam'iyyun da za a kafa gwamnatin hadakar  tare da su.

 Har yanzu shugabannin jam'iyyar SPD na ci gaba da tallan batun hadakar ga sauran 'yan jam'iyyar, kuma nan gaba za su yi babban taro a birnin Bonn don duba yiwuwar amincewa da shi ko akasin haka. Kafa gwamnati dai ita ce kadai hanyar da za ta sa a kauce wa kafa gwamnatin marasa rinjaye ko kuma a sake sabon zabe a Jamus.