Merkel ta bukaci sulhunta rikicin Hong Kong | Labarai | DW | 06.09.2019
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Merkel ta bukaci sulhunta rikicin Hong Kong

Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta jaddada bukatar martaba 'yancin al'ummar Hong Kong bayan da ta gana da Firmiyan Chaina Li Keqiang a birnin Beijin

Merkel wadda ke ziyarar kwanaki uku a Chaina ta ce ta tattauna da mahukuntan kasar game da tashin hankalin da fama da shi a yankin Hong Kong inda ta nemi a sulhunta takaddamar cikin ruwan sanyi tsakanin gwamnati da masu zanga zanga

A ranar alhamis Merkel ta sauka Chaina tare da rakiyar 'yan kasuwar Jamus masu tarin yawa da kuma kamfanoni da suka hada da kamfanin kera motoci na Volkswagen.

Shugabar gwamnatin ta Jamus a yayin da ta ke tattaunawa da shugaban Chaina Xi Jinping ta jaddada bukatar sanun masalaha a rikicin kasuwanci tsakanin Chaina da Amirka tana mai cewa rikicin da ya kunno kai tsakanin kasashen biyu na matukar tasiri akan sauran kasashen duniya.


Chaina dai ta kasance babbar abokiyar kasuwancin Jamus inda a shekarar 2018 suka yi ciniki na kimanin euro miliyan 200