Merkel na cikin tsaka mai wuya | Labarai | DW | 12.07.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Merkel na cikin tsaka mai wuya

Watanni kalilan gabanin babban zabe a nan Jamus, shugabar gwamnati Angela Merklel na fuskantar suka bisa goyon bayan tatsar bayanan siriin jama'a da ta yi.

Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel na fuskantar suka, dangane da goyon bayan shirin tatsar bayanan sirrin jama'a da Amirka keyi a asirce, wanda ta bayyana da wani matakin kare kai daga aiyukan ta'addanci.

A farkon wannan mako ne dai Merkel, ta bayyana cewa babu wani banbanci tsakanin aikin da 'yan sandan sirri na tsohuwar gabashin Jamus suka yi da kuma wanda Hukumar Tsaron Amirka keyi na tatsar bayanan sirrin jama'a a asirce.

Wannan bayani na ta dai na zuwa ne a dai dai lokacin da ministan cikin gida na nan Jamus ya nufi birnin Washington, domin ganawa da mai baiwa shugaban Amirka Barack Obama shawara kan al'amuran tsaro Lisa Monaco, inda ake kyautata zaton za su tattauna batun leken asirin da aka ce Amirkan na yi wa Jamus da sauran kasashen nahiyar Turai.

Mawallafiya: Lateefa Mustapha Ja'afar
Edita: Umaru Aliyu