1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Merkel- Ina kula da lafiyata sosai

Mohammad Nasiru Awal AMA
July 20, 2019

Merkel ta kwashe tsawon mintuna 90 tana amsa tambayoyin manema labarai a Berlin kan batutuwa da dama ciki har da na lafiyarta.

https://p.dw.com/p/3MQUX
Angela Merkel Sommerpressekonferenz Berlin
Hoto: Reuters/H. Hanschke

Bayan fadi tashi na makonnin baya bayan nan shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta shirya tsaf don fara hutunta na lokacin zafi. Amma bisa al'ada kafin wannan hutu a kowace shekara ta kan amsa tambayoyin 'yan jarida da ke birnin Berlin fadar gwamnatin Jamus. Bisa ga dukkan alamu ta gamsu da yadda ministar tsaronta Ursula von der Leyen ta yi nasarar darewa kan kujerar shugaban hukumar tarayyar Turai EU, kamar yadda kalaman Merkel suka nunar.

"Ita ce mace ta farko da za ta jagoranci hukumar EU. Ina kuma farin ciki da haka ya kai ga kauce wa wani fito na fito a cikin hukumomin Turai. Haka ya nuna karara EU na karfin dinke baraka a cikinta."

Ko da yake batun siyasar cikin gida ya dauki hankali a zauren taron manema labaran, amma kuma an saka kunne don jin bayaninta game da manufofinta na ketare. Ta ce a shirye take ta ga an samu daidaito dangane da batun ficewar Birtaniya daga EU.

"Idan Birtaniya na bukatar karin lokaci, za mu ba ta wannan lokaci, idan ba ta bukatar wannan lokaci, muma ba ma bukatar mu ce komai kan wannan batu."

Greta Thunberg jagorar gangamin "Fridays For Future" lokacin wani gangami a Berlin
Greta Thunberg jagorar gangamin "Fridays For Future" lokacin wani gangami a BerlinHoto: Reuters/F. Bensch

Yayin da take amsa tambayoyin a waje 'yan mitoci kadan daga zauren taron manema labaran, 'yan makaranta ne karkashin jagorancin matashiyar nan 'yan kasar Sweden da ta shahara wajen yaki da dumamar yanayi karkashin taken "Fridays For Future da a kowace Jumma'a suke gangamin yaki da dumamar yanayi, suka hallara. Merkel ta goyi bayan gangamin.

"Jajircewar da matashiyar Greta Thunberg da takwarorinta matasa suka yi suna jawo hankalinmu cewa rayuwarsu da kuma makomarsu ce, ya kara karfafa mana gwiwa na daukar matakan da suka dace."

Da ta juya kan batun lafiyarta musamman yadda a makonnin baya-bayan take ta karkarwa a bainar jama'a, da ke saka ayar tambaya ko tana da cikakken koshin lafiyar ci gaba da aiki a matsayin shugabar gwamnati, Merkel cewa ta yi:

"Zan iya ci gaba aikina na shugabar gwamnati, zan kuma maimaita bayanin da na yi baya-bayan nan cewa a matsayin dan Adam ina da babbar sha'awa ta kula da lafiyata. Shekarar 2021 za ta kasance shekarar da zan yi ban-kwana da siyasa. Akwai wata rayuwa bayan siyasa, ina kuma fata zan yi ta cikin koshin lafiya."

Duk da hutun ta ce a kullum tana cikin aiki ne ana kuma iya samunta ta waya idan da bukata.