1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Merkel da Sarkozy sun cimma matsaya game da rikicin Euro

Mohammad AwalJanuary 9, 2012

Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta gana da shugaban ƙasar Faransa Nicolas Sarkozy a birnin Berlin, a inda suka fahimci juna game da matakan da ya kamata a ɗauka domin kawo ƙarshen matsalar kuɗi a nahiyar Turai.

https://p.dw.com/p/13gd2
Bundeskanzlerin Angela Merkel (CDU) empfaengt am Montag (09.01.12) vor dem Bundeskanzleramt in Berlin den franzoesischen Praesidenten Nicolas Sarkozy. Die beiden Staatsoberhaeupter kommen zu einem gemeinsamen Mittagessen zusammen. (zu dapd-Text) Foto: Axel Schmidt/dapd
Merkel da Sarkozy suka ce babu ja da baya game da rikicin Euro.Hoto: dapd

Merkel da Sarkozy sun yi fatan ganin mambobi 26 daga cikin 27 na EU sun rattaɓa hannu akan yarjejeniyar da za ta bayar da damar kyautata tsarin kasafin kuɗi a ƙasashen Turai a ranar ɗaya ga watan maris mai zuwa. shugabannin na ƙasashen Jamus da kuma Faransa sun amince za su zurfafa tunani game da yadda za su hanzarta zuba kuɗin karo karo a asusun ko ta kwana na ƙasashen EU. Hakazalika sun jaddada aniyarsu na ci gaba da damawa da Girka a cikin ruƙunin ƙasashen da ke amfani da takardar kuɗin Euro, bisa sharadin cewa ƙasar da ke fama da matsin tattalin arzuki za ta ci gaba da tsuke bakin aljuhunta, tare da aiwatar da sauye sauye a fannin tattalin arziki.

Merkel da Sarkozy sun kuma bayyana cewar sun nemi gudunmawar babban bankin Turai domin ta ƙarfafa tsarin da suka girka wanda ya kasa biyan kudin sabulu, wato ƙwarya ƙwaryan tsarin nan na tallafa ma ƙasashe Eu da ke fama da matsalar ƙarancin kuɗi. Dukkaninsu biyu, sun dage akan ganin cewa tsuke bakin aljuhu da ƙasashe da ke amfani da Euro ke yi bai haddasa koma baya ko ƙarancin ayyukan yi a cikinsu ba. A cewar shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel, waɗannan matakai babban ci gaba ne a yunƙurin shawo kan matsalar kuɗin Euro.

Bundeskanzlerin Angela Merkel (CDU) und der franzoesische Praesident Nicolas Sarkozy kommen am Montag (09.01.12) waehrend eines Treffens im Bundeskanzleramt in Berlin zu einer Pressekonferenz. Bundeskanzlerin Angela Merkel und Frankreichs Staatspraesident Nicolas Sarkozy machen Druck fuer die Einfuehrung einer Finanztransaktionssteuer. Merkel sagte am Montag nach einem Treffen mit Sarkozy in Berlin, sie persoenlich koenne sich eine solche Abgabe auch auf Ebene der Euro-Laender vorstellen, auch wenn es dazu noch keine Einigung in der Bundesregierung gebe. (zu dapd-Text) Foto: Axel Schmidt/dapd
Merkel da Sarkozy sun yi bayyani a taron manaima labarai.Hoto: dapd

"Da farko dai abin farin ciki na ganin cewa tattaunawa game da rikicin kuɗi ya kama hanyar biyan kuɗin sabulu. Akwai alamun cimma matsaya game da matsalar ta kuɗi da ma sauran matsalolin a wannan wata na janairu, da kuma watan maris. Ina ganin cewar Jamus da kuma Faransa sun kawo ci gaba da mai ma'ana."

Shugabar gwamnatin ta Jamus ta yi na'am da tsarin da Sarkozy ya ke da niyar ɓullo da shi na ƙaƙaba haraji akan hada hadar kuɗaɗe a ƙasar Faransa. Sai dai Angela Merkel ta na so akasarin ƙasashe mambobin Eu sun amince da tsarin kafin a aiwatar da shi a Jamus da ma dai sauran ƙasashe na EU. Amma kuma Nicolas Sarkozy ya nunar da cewa a ƙarshen wannan wata na janairu ne gwamnatinsa za ta shigar da daftarin gaba majalisa domin nazari tare da albarkanta. Sai dai sarkozy ya yaba irin haɗa ƙarfi da ƙarfe da ƙasashen na Jamus da Faransa suka yi domin laluɓo hanyoyin warware matsalar kuɗi da ke addabar nahiyar Turai.

"Ina so in miƙa godiya ta ga shugabar gwamnati Angela Merkel dangane da wannan aiki na hadin guywa da muke gudanarwa tsakanin Faransa da Jamus. Burin da muka sa a gaba, shi ne gudu tare domin tsirar da takardar kuɗin Euro daga wannan rikici na kuɗi da ya addabe ta."

French President Nicolas Sarkozy (R) and German Chancellor Angela Merkel shake hands after a news conference following their talks at the Chancellery in Berlin January 9, 2012. REUTERS/Fabrizio Bensch (GERMANY - Tags: POLITICS)
Merkel da Sarkozy za su cin gaba da gudu tare...Hoto: Reuters

A ranar talatin ga wannan wata na janairu ne za a gudanar da taron ƙolin na shugabannin Eu a cibiyarta da ke Bruxelless na Beljium. Wannan taro da ba shi ne irinsa na farko ba, zai mayar da hanakali ne kan hanyoyin ceto tattalin arzikin ƙasashen da ke amfani da Euro daga mummunan hali da ya shiga.

Mawallafi: Mouhamadou
Edita: Ahmad Tijjani Lawal