Merkel da Hariri sun gana a birnin Berlin | Labarai | DW | 15.03.2010
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Merkel da Hariri sun gana a birnin Berlin

Angela Merkel ta baiyana fatan Isra´ila zata kawo ƙarshen gine- gine a yankunan Palestinawa

default

An tattauna tsakanin Merkel da Hariri a birnin Berlin

Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel tayi suka ga shirin Isra´ila na cigaba da gine-gine a yankunan Palasɗinawa. A ganawar da tayi da Firaministan Lebanon Saad Hariri a birnin Berlin, Merkel ta baiyana fatan Isra´ila zata kawo ƙarshen matakan daka iya takawa shirin zaman lafiyan yankin Gabas ta Tsakiya birki. A ɓangaren sa, Hariri yayi fatan samun zaman lafiya a yankin inda yace: samun zaman lafiyan Palasɗinawan zai taimaka wajen cigaban ƙasar Lebanon da kuma yankin baki ɗaya, don haka ako yaushe ƙawayenmu suka tambaye mu yadda zasu taimaka mana, muna baiyana masu buƙatar samun zaman lafiya a Palasɗinu . Aniyar Isra´ila taci gaba da gina gidajen yahudawa a yankunan Palasɗinawa na fuskantar suka daga ƙasashen duniya musamman babbar ƙawar Isra´ilan Amirka. Jakadan Isra´ila a birnin Washington yace wannan matsala itace mafi tsanani da Isra'ilan ke fuskanta tun bayan rikicin shekarar 1975. Tuni dai hukumomin Palasɗinu suka baiyana ƙauracewa tattaunawar zaman lafiyan muddin Isra´ila taci gaba da shirin gina matsugunan na yahudawa. A makon jiya ne dai Isra'ila ta baiyana cigaba da gina sabbin matsugunan Yahudawa a yankunan Palasɗinawa. Matakin da yanzu haka yake fuskantar suka daga ƙasashen duniya daban-daban, da suka haɗa da Amirka da kuma ƙungiyar Tarayyar Turai.

Mawwallafi:Babangida Jibril Edita: Yahouza Sadissou Madobi