1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jawabin Angela Merkel ya maida hankali kan annobar corona

Lateefa Mustapha Ja'afar AMA
December 31, 2020

Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel, ta nemi hadin kan al'umma wajen yakar annobar coronavirus a yayin jawabinta da ta saba gabatarwa na sabuwar shekara.

https://p.dw.com/p/3nPff
Deutschland Neujahransprache der Kanzlerin | Angela Merkel
Angela Merkel na jawabin shiga sabuwar shekara ta 2021Hoto: Markus Schreiber/REUTERS

A jawabin nata, shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel, ta fara ne da cewa: Shekara ta 2020 ta zo da ban mamaki, abin da duniya ba ta tsammata ba. Wata kwayar cuta ta shige jikinmu da rayuwarmu. Ta sanya mu zaman dar-dar a wajen haduwa da rungmar juna da tataunawa da ma bukukuwa. Merkel ta nunar da cewa al'ummar kasarta sun nuna juriya matuka dangane da yadda mahukun ta suka yi ta tsawaita bukatarsu ta neman amincewarsu, da kuma hakuri kan ka'idoji da dokokin da suke shimfidawa wajen yakar wannan annoba, inda ta nuna alhininta tana mai cewa "A karshen wannan shekara da ta han mu shakar numfashi, muna juriya da jimamai. Mu a matsayinmu na hukuma bai kamata mu manta da yaawan mutanen da suka rasa rayukansu ba, da ba za mu ga karshen wannan shekarar da su ba. Ba zan iya dauke muku zafin rashin da kuka yi ba, amma ina shaida muku kuna cikin raina har ma a wannan yammacin." Da ta ke kara jaddada muhimmancin bin ka'idoji, Merkel ta nunar da cewa ba domin al'umma sun ba yar da hadin kai ba, da ba a kai ga cimma nasarar da aka samu kawo yanzu ba.

Karin Bayani: An yi tir da masu bore da matakan yaki da Covid-19

Fatan ganin allurar rigakafin corona ta kawo karshen annobar

Schweitz Corona-Impfung in Luzern
Ana yi wa wata tsohuwa allurar rigakafiHoto: Urs Flueeler/Keystone/Kanton Luzern/REUTERS

A ranar 27 ga wannan wata na Disamban 2020 ne aka fara gudanar da allurar rigakafin cutar ta coronavirus a Jamus da kuma sauran kasashen kugiyar Tarayyar Tura, Shugabar Gwamnatin Jamus Angela Merkel ta nunar da cewa rigakafin ta haifar da kyakkyawan fatan gainin karshen annobar, inda ta ce "An fara gudanar da alurar rigakafi ga wasu tsofaffi da kuma wasu ma'aikatan lafiya da ke kula da su da kuma ma'aikatan da ke dakin kula da marasa lafiyar da ke cikin halin rai kwakwai mutu kwakwai. Ba a nan kadai ba, a kasashen nahiyar Turai baki daya. A kowacce rana ana yi wa mutane allurar rigakafin, nima in ina cikin wannan rukuni, zan je a yi min."

Karin Bayani: Coronavirus ta barke a wata mayanka

Ta kara da cewa, annobar coronavirus ta kasance wani al'amari da ya shafi siyasa da zamantakewa da ma tattalin arzikin karni a tarihin shekaru aru-aru, tana mai cewa matsala ce babba a tarihin duniya da ta shafi al'ummomi da al'amura ma su yawa inda ta ce "Ina tunanin ba zai kasance zuzutawa ba idan na ce cikin shekaru 15 din da suka gabata, ba mu tsinci kanmu cikin damuwa kamar wannan shekarar ba, duk kuwa da tarin matasalolin da duniya ke ciki, sai dai duk da haka mutane da na kyakkyawan fata. Ina yi wa dukkanin al'umma fatan lafiya da juriya da kuma albarkar Allah a sabuwar shekara ta 2021."

Nuna alhini kan wadanda suka rasa 'yan uwansu da Covid-19

Karikatur | Sergey Elkin | Lockdown Deutschland
Hoton barkwanci na yaki da coronavirusHoto: Sergey Elkin

Shugabar Gwamnatin Jamus Angela Merkel, ta ce za ta iya hasashen halin da wadanda ska rasa 'yan uwansu sakamakon wannan anoba suka shiga ne kawai da ma wadanda suke fama da wata lalura bayan sun yi fama da annobar sun kuma fi karfinta. Da ta ke bayyana takaicinta kan masu yada shaci fadi, Merkel ta ce wannan dabi'a ba wai kawai karya bace, amma nuna rashin imanin ne ga al'umma.