Merkel ba ta dauke da cutar coronavirus | Labarai | DW | 23.03.2020
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Merkel ba ta dauke da cutar coronavirus

Binciken farko da aka gudanar game da yiwuwar ko ta harbu da kwayoyin cutar Corona ya yi nuni da cewar shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel bata kamu da kwayar cutar ba duk da ganawar da likitan da ke dauke da cutar.

Tun daga farko kakakinta ya ce shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel na nan lafiya kalau kana kuma tana ci gaba da aikinta a gida bayan ta killace kanta, sannan ya ce za a ci gaba da sauran gwaje-gwaje nan da gaba kan shugabar gwamnati, bayan binciken farko ya nuna cewa bata dauke da kwayoyin cutar.

Da sanyin safuyar yau Litinin shugabar gwamnatin ta halarci wani taron majalisar minitocin kasar ta wayar tarho inda gwamnatin ta dauki wasu muhimman matakai game da batun tattalin arziki.

Kawo yanzu fiye da mutun dubu 22 da 670 ne suka harbu da cutar a Jamus wasu 86 suka rigamu gidan gaskiya a cewar wata cibiar bincike ta Robert Koch Institut.