Menene Fargar Jaji | Amsoshin takardunku | DW | 16.07.2007
 1. Inhalt
 2. Navigation
 3. Weitere Inhalte
 4. Metanavigation
 5. Suche
 6. Choose from 30 Languages

Amsoshin takardunku

Menene Fargar Jaji

Bayani game da ma'anar Fargar Jaji

Sarki Ado da Sarauniyar Ingila

Sarki Ado da Sarauniyar Ingila

Jama’a masu sauraronmu assalamu alaikum, barkammu da wannan lokaci, barkammu kuma da sake saduwa da ku a cikin wani sabon shirin na amsoshin takardunku,shirin da yake amsa tambayoyin da ku masu sauraro kukan aikomana.

Halima: Fatawarmu ta wannan makon ta fito daga hannun mai sauraronmu a yau da kullum, Malam Bawa Haladu, Birnin Gwari, Kaduna , Najeriya;Malamin cewa yayi; Shin me yasa ake yiwa Bahaushe kirari da cewa “Bahaushe Jikan Jaji’’. Kuma menene alakar wannan kirari da karin maganar nan na“Fargar Jaji

Bashir: To mun mika wannan tambaya ta Malam Bawa Haladu , ga Malam yakubu Azare, malami a sashen harsunan Najeriya, a Jami’ar Bayero dake Jihar Kanon Tarayyar Najeriya. Ga kuma abinda ya ce dangane da amsar wannan tambaya.

Azare: To wannan karin magana na fargar Jaji, ya samo asali ne daga wani Mutum da ake kira Jaji, wanda yayi zamaninsa tun tale-tale. Shi dai Jaji mayaki ne kuma Jarumi ne. Ya kasance yana da layar bata, wadda idan yaga rana zata baci a gare shi, to sai ya matsa wannan laya ya bace. To ananan wata rana sai gumu tai gumu, yaki yai yaki tsakanin Jaji da abokan gaba. Jaji bai farga cewar yana da layar bata ba sai da ya ji takobi a wuyansa sannan ya tuna sai ya matsa layar tasa, yana matsata kuwa sai gangar jikinsa ta bace amma kuma kansa sai ya fadi gefe guda,wato dai kafin ya gama matsa layar an fille masa kai.

To wannan kuskure da Jaji yayi na rashin farga da wuri a lokacin da take da amfani, sai bayan da lokaci ya kure, wato lokacin da fargar tasa bazata amfane shi ba , shi yasa Bahaushe ya kirkiri karin maganar fargar jaji. Kuma kasancewar Malam bahaushe yana da dabi’a irin ta Kakansa jaji na rashin tuna abu da wuri a lokacin amfaninsa shi yasa ake yiwa Bahaushe kirari da cewa Bahaushe jikan Jaji.

Bashir: Wannan batu yana nuna cewa, akwai sakaci da lalaci a rayuwar Malam Bahaushe, wadda tasa ake barin sa a baya a cikin gwagwarmayar rayuwa, musamman ma a wannan zamani, me zaka ce game da wannan?

Azare: Babu shakka kowa yasan cewa Malam bahaushe idan aka yi la’akari da rayuwar makotansa ,to sai ace yana da sakaci wajen gwagwarmayar rayuwa, musammam madai yadda idan Malam bahaushe ya samu wani matsayi ko wata daukaka to sai ya manta da danginsa da yan-uwansa da sauran jama’a, daga shi sai Iyalinsa, koda kuwa mukami ne na hukuma wadda talakawa da sauran jama’a suke da hakki a ciki. To amma ba duka aka taru aka zama daya ba , akwai hausawa da dama wadanda suka kasance gwarzaye, wadanda suka tsaya tsayin daka wajen tabbatar da adalci da yancin al’ummarsu. To irin wadannan Hausawan sune Hausawa na-gari wadanda ake so ko wanne Bahaushe yayi koyi dasu. Haka zalika ba Bahaushe ne kawai yake da irin wannan sakaci ba, akwai Kabilu da dama a wannan duniya da suke da irin wannan dabi’a ta fargar Jaji.

 • Kwanan wata 16.07.2007
 • Mawallafi Abba Bashir
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink https://p.dw.com/p/BvUo
 • Kwanan wata 16.07.2007
 • Mawallafi Abba Bashir
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink https://p.dw.com/p/BvUo