Muna amfani da "Cookies" domin inganta abubuwan da muke wallafawa a intanet. Za ku iya samun karin bayani a kundin kare bayananmu.
Shirin ya kunshi rahotanni da labarai daga sassan duniya dama rahotonmu na musanman kan hobbasar da matasa ke yi na samar wa kansu aiyukan dogaro da kai. Zuwa sauti
Bayan labaran duniya, a cikin shirin za a ji yadda ake kokawa kan halin matsin rayuwa da ake ciki a tarayyar Najeriya. Zuwa sauti
Kungiyoyin agaji na duniya, na gargadi kan yiwuwar matsalar yunwar da wahalhalu da ake ciki a yankin kusurwar Afirka ta karu. Farashin kayan abinci ya yi tashin gwauron zabi. Zuwa sauti
Za a ji hukumomi sun tabbatar da mutuwar mutane da jikkatar wasu a fashewar tukwanen gas a jihar Kano a Najeriya.
Shirin wannan lokaci ya dubi yadda ake mutunta juna ne a yankuna na Najeriya, inda ake bai wa wadanda ba 'yan asali ba mukamai a wasu yankuna na kasar. Mun yi nazari ne musamman a yankin kudanci kasar.
A cikin shirin za a ji cewa a Najeriya al’amurra sun soma daidaita kamar yadda aka saba yau da kullum a jihar Sakkwato, bayan sassauta dokar hana fita ta sa’o’i 24 da gwamnan jihar ya kakaba., a daidai lokacin da wata sabuwar kungiyar 'yan bindiga ta bulla a jahar Rivers, bisa manufar fara tada hankali a sassan yankin Niger Delta.
Yayin da zabukan 2023 ke matsowa, guguwar sauyin sheka a jam'iyyar APC da rashin tabbas ga jam'iyyar PDP na ci gaba da kawo rudani a siyasar jihar Kano a Najeriya.
Akalla fararen hula 20 ne aka kashe a makon da ya gabata a garin Ituri da ke arewa maso gabashin Jamhuriyar Dimukaradiyyar Kwango, a wani hari da ake dangantawa da na ‘yan tawayen ADF (Allied Democratic Forces).
A cikin shirin za a ji cewa a Jamhuriyar Nijar 'yan siyasa ne ke tofa albarkacin bakinsu kan matakin kasar Mali na ficewa daga kungiyar G5 Sahel da ma rundunar hadin gwiwa ta yaki da ta'addanci a yankin. A Saliyo kuwa, gwamnati ce tafara daukar mataki kan masu tallace-tallace da sifiku a kan hanya.
Shirin ya dubi yanda mata da dama suka dauki zama da kishiya wani babban al'amari mara sauki. Mata dai kan ta da hankali idan aka yi batun kishiya.
Ko kun san tarihin yadda Hadaddiyar Daular Larabawa ta dunkule ta zama DUBAI a halin yanzu? Ku saurari yadda labarin yake a bayanan da Mahmud Yaya Azare ya yi.
A cikin shirin za a ji cewa masana da kungiyoyin kare muhalli daga sassa daban-daban na Afirka na ci gaba da jinjinawa taken taron kare muhalli na bana Cop15 da ake gudanarwa, a yayin da hukumar kula da kare hakin masu amfani da makamashi ta kamalla wani taron waye kan wakillan al'umma da jagororin kamfanonin wutar lantaki a Jamhuriyar Nijar.
Bayan Labaran Duniya akwai shirin Ra'ayin Malamai da shirin Amsoshin Takardunku.
Za a ji yadda daruruwan masu zanga-zanga suka fito nuna adawa da gwamnatin kasar Tunisiya
Za a ji yadda tsarin iyali yake gudana tsakanin mazauna birane da karkara
Bayan Labaran Duniya akwai shirin Ji Ka karu da shirin Darasin Rayuwa da ma na Ra'ayin Malamai.
Za a ji yadda yadda gwamnatin Ukraine ke ikirarin cewa sojojin Rasha suna janyewa daga gabashin Donbas
Za a ji bitar wasu muhimman rahotanni da suka dauki hankali a mako mai karewa a nahiyar Afirka
A cikin shirin za a ji cewa a Najeriya kungiyar Miyatti Allah ta Fulani makiyaya ta bayyana damuwa a kan sabbin kasha-kashen da ake yiwa ‘ya'yanta a yankin Kudu maso gabashin kasar.