Muna amfani da "Cookies" domin inganta abubuwan da muke wallafawa a intanet. Za ku iya samun karin bayani a kundin kare bayananmu.
A cikin shirin za aji cewa a karo na shida a cikin shekaru 35 shugaban Yuganda ya lashe zaben shugaban kasa, a Najeriya kuwa an kammala zabukan kananan hukumomin jihar Kano 44 wanda jamiyyar APC mai mulki ta lashe zaben.
Jagoran adawa a kasar Yuganda Bobi Wine yace sojoji sun shiga sun kuma karbe iko da gidansa yana mai cewa yana cikin hadari.
Matasa masu kanana sana'o'i da ke da sana'oinsu ta shafukan sada zumunta a nahiyar Afirka, sun samu kansu cikin matsi da wasu karin kalubale sakamakon tsadar Data. Duk da cewa an samu damar yin kasuwanci ta kafar Internet, sakamakon dokar kulle saboda dakile yaduwar annobar corona, matsalar ta yi kamari a Yuganda.
Sana'o'in hannu musamman ga matasa, abubuwa ne da sannu a hankali suke karbuwa a nahiyar Afirka, domin kuwa a yanzu matasan wannan nahiya sun tashi tsaye wajen koyo da ma koyar da sana'o'in dogaro da kai.
Cikin shirin za ku ji yadda Hukumomi a Yuganda suka shirya rarraba wa ‘yan kasar takunkumin kare baki da hanci saboda kauce wa kamuwa da cutar corona.
Rawar da gwamnatin Birtaniya ta taka wajen hana a saka wa Najeriya takunkumin sayar dai mai, a zamanin mulkin marigaye janar Sani Abacha da batun bunkasar tattalin arzikin kasar Ruwanda na cikin muhimman batutuwan da suka dauki hankalin jaridun Jamus a wannan mako a sharhunan da suka rubuta kan nahiyar Afirka.
A Jamhuriyar Nijar dubban mutane sun bar matsugunnansu a yankin garin Chinegodar, inda ‘yan ta’adda suka kai harin da ya yi sanadiyyar mutuwar sojojin kasar 89.
Cikin hsarhin da ta yi jaridar Süddeutsche Zeitung wadda ta ce matashin nan dan salon wakar rap Bobi Wine ya zame wa manyan masu mulki a kasar Yuganda ala-kakai kasancewa yana samun nasara fiye da 'yan siyasa.
A Kasar Yuganda dubban matasa ne ke son shiga aikin soja a matsayin wata hanyar samun makoma a rayuwarsu. Ga misali a lokacin da ake bukatar daukar sojoji 4000, amma kimanin matasa maza da mata 10000 ne ke zuwa don samun a dauke su.
A cikin shirin za ku ji cewar a kasar Yuganda, an cafke fitaccen mawakin nan Bobi Wine da ke adawa da shugaba mai ci Yoweri Museveni.
A cikin shirin za kuji cewa: 'Yan tawayen ADF da ke dasawa da Yuganda sun kai hari a garin Beni da ke gabashin Jamhuriyar Dimukaradiyya Kwango inda suka kona gidaje da dama tare da salwantar da rayukan mutanen garin.
A Yuganda mafarkin masu albashi maras tsoka na samun mota na nesa ga cika sakamakon dokar da gwamnatin ta bullo da ita ta haramta shigo da tsoffin motoci na tuwarist da suka wucce shekaru 15 da kerawa.
A cikin shirin bayan Labaran Duniya, muna tafe da rahoto kan hama shigar da tsofaffin motoci kasar Yuganda. Akwai sauran rahotanni da kuma shirye-shiryen da muka saba gabatar muku.
Masana kimiya sun baiyana damuwa game da yawaitar adadin masu fama da cutar HIV/AIDS a kasar Yuganda.
A karon farko madinka daga kasashen Senegal Yuganda da Benin sun baje kolin tufafi da sauran kayan kwalliya na Afirka a birnin Berlin. Wannan rukunin madinkan na Afirka na zamani na da burin daukaka martabar tufafin Afirka da sauya tunanin da duniya take da shi na fifita tufafin Turai idan ana maganar ado da kwalisa.
Amirka ta dankara takunkumi kan Turkiyya sakamakon afkawa kasar Siriya
A cikin shirin bayan Labaran Duniya, muna tafe rahoto kan halin da 'yan gudun hijirar Libiya ke ciki a Ruwanada, akwai sauran rahotanni da shirye-shiryen da muka saba gabatar muku.
A Najeriya Shugaba Muhammadu Buhari ya rantsar da sabbin ministocinsa. Kasashen Ruwanda da Yuganda sun kulla yarjejeniyar fahimtar juna.
Za kuji cewar kakakin hukumar 'yan sandan kasar Yuganda Fred Enanga ya bayyana karya dokar tsaron kasa a matsayin dalilin da sanya jami'an tsaro suka kame shahararren mawaki kuma mai adawa Bobi Wine.
An dai sani akwai fahimta tsakanin Yoweri Museveni na Yuganda da takwaransa Paul Kagame na Ruwanda, amma an rufe iyakar kasashen biyu, hanyar da miliyoyin 'yan kasuwa da al'umma ke bi don hulda tsakanin kasashen.