Muna amfani da "Cookies" domin inganta abubuwan da muke wallafawa a intanet. Za ku iya samun karin bayani a kundin kare bayananmu.
Bayan labaran duniya, za a ji cewa Najeriya ta daga haramcin yin rijistar layukan waya a kasar, matakin da ta ce ta dauka ne domin magance matsalar tsaro da ya zame wa kasar karfen kafa.
Gwamnatin tarrayar Najeriya ta dage haramcin rijistar wayar salula a kasar. Mahukunta na Abuja sun ambato batun rashin tsaro a kan gaba a cikin matakin tsaida rijistar katin na salula.
Cikin Shirin za a ji yanda dubban 'yan gudun hijiran garin Damasak ke shiga Jamhuriyar Nijar. A Najeriya gwamnatin Katsina ta fara amfani da karnuka wajen tsare makarantu. A Taraba sojoji ne suka kashe wasu matasan da ba su ji ba ba su gani ba.
A wani mataki na taimaka wa mazauna karkara da ke fama da matsalar lalacewar injin nika mai amfani da ruwa wajen sarrafa gero ko masara, Issoufou Ousmane ya rungumi sana’ar gyaran tahuna mai aiki da ruwa ko wutar lantarki.
Jamhuriyar Afirka ta tsakiya na fama da kalubalen rashin tsaro, inda 'yan tawaye ke ci gaba da gwabza fada da dakarun gwamnati.
Bukatar makamashi na karuwa a Afirka, inda yanzu haka wasu gwamnatoci a nahiyar suka karkata ga gina tashoshin samar da makamashi daga kwal.
Yayin da Musulmi a duniya ke haramar fara azumin watan Ramadana, a Najeriya da Nijar jama'a na fama ne da matsalolin tsaro da annobar corona. Najeriya ta kaddamar da neman sama da mutane 3400 da suka tsere daga gidajen yari da ofisoshin 'yan sanda a kudancin kasar.
Matasa a nahiyar Afirka na fuskantar matsalar rashin aikin yi. Hakan ce ta asanya a yanzu haka matasan ke tashi tsaye domin neman na kansu ta hanyar kama kanana da matsakaitan sana'o'i.
Za a ji kamfanin Total na Faransa ya dakatar da aiki a arewacin Mozambik saboda barazanar tsaro
Cikin shirin za a ji yadda kungiyoyin kare hakki da ma lauyoyi ke gargadi a kan yadda ake yi wa Fulanin kasar kudin goro a game da matsalar garkuwa da mutane. A Kamaru akwai shirin gwamnati na wajabta rigakafi a kan dukkanin 'yan kasa.
A Najeriya wasu kungiyoyin kare hakkin jama’a da na Fulani, sun fara wani yunkuri neman kawo karshen matsalar tsangwama da nuna duk wani bafulatani makiyayi a matsayin mai garkuwa da jama’a da satar shannu a kasar,
Masu karamin karfi a Ruwanda na baiyana fargabar karuwar cin zarafin mata bayan umarnin gwamnati na soke dokar da ta dauke wa mata biyan kudin shigar da kara.
A wani yunkuri na magance matsalar yaduwar corona, wasu daliban makarantar sakandare ta Glisten da ke Abuja sun kirkiri mutum-mutumi mai aiki da na'ura don agaza wa marasa lafiya wajen kai magani da kuma kula da zafin jikinsu.
A cikin shirin za a ji tasirin tabarbarewar tsaro da ya fara shafar tattalin arziki a Najeriya.
An bude taron kasa da kasa don inganta tsaro da zamantakewa tsakanin al'ummar yankin Sahel da Tabkin Chadi
A cikin shirin za a ji cewa shekaru 10 kenan da Kungiyar Kawancen Tsaro ta NATO ta tallafa wa 'yan tawayen kasar Libiya wadanda suka tayar da kayar baya wa tsohon shugaban kasar Muammar al-Gaddafi kayar baya, a yayin da 'yan adawa suka nace da ci gaban zanga-zangar kin jinin adawa da sakamakon zabe.
A shekarar 2011, shekara 10 ke nan da kungiyar kawancen tsaro ta NATO ta tallafawa kungiyoyin tawayen kasar Libiya, wadanda suka tayarwa tsohon shugaban kasa Marigayi Muammar Gaddafi kayar baya.
‘Yan sanda a Najeriya sun hana zanga-zangar neman mahukunta su dauki mataki a kan matsalar sauyin yanayi wadda ake yi domin jawo hankalin hukumomi su dauki mataki.