Muna amfani da "Cookies" domin inganta abubuwan da muke wallafawa a intanet. Za ku iya samun karin bayani a kundin kare bayananmu.
Wata cuta da ke damun mata masu shekaru na karkara Agadez da ke Jamhuriyar Nijar ita ce cutar fitsari.
A birnin Agadez na Jamhuriyar Nijar, hadakar kungiyoyin addinai sun bayar da horo ga sarakunan gargajiya da malamai da kuma mata dangane da kyautata zamantakewa a tsakanin al'umma domin a samun zaman lafiya. Ku saurari shirin Taba Ka Lashe.
Ko kun san irin rawar da mata ke takawa a fannin siyasa da ma fatan da suke da shi a al'amuran da suka shafi siyasar a Jamuhuriyar Nijar? Shirin Abu Namu ya amsa wadannan tambayoyi.
A cikin shirin bayan labaran duniya za ku ji irin mawuyacin halin da mata suka ce rikicn ‘yan bindiga ya jefa su a Sokoton Najeriya. Akwai rahoto kan yadda yankin Diffa ke fama da rashin tsaro shekaru 10 da mulkin PNDS Tarayya a Nijar. A Kamaru DW ta duba yadda rikicin ‘yan aware ya tagayyara dalibai.
A cikin shirin likitocin sun yi bayani kan cutar da ke kama mata bayan haihuwa wato Eclampsia a Turance ko kuma cutar Taune-Taune da Hausa. Sai kuma bayani kan cutar da ke sanya sata wadda ake kira Klaptamenia a Turance.
Wani matashi da yake sana'ar yi wa mata kwalliya, ya shahara tsakanin takwarorin sa a Jihar Adamawa a Najeriya inda mata da 'yan mata ke zuwa kai a kai a shagon sa domin yin kwalliya.
Sana'ar dafa indomi ya ci gaba da samun bunkasa fiye da duk wani lokaci a kasar Ghana, a sakamakon yadda matasa maza da mata suka rungumi wannan sana'a don samun abin rufin asiri.
Rashin samun auduga don amfani a lokacin jinin al'ada ya janyo koma baya matuka ga ilimin yara mata, musamman ga wadanda ke rayuwa a yankunan karkara a kasashen duniya masu tasowa.
Wasu iyaye da dama, ba sa son shayar da jariransu nono uwa. Shin ko me yake janyo hakan? Shirin Lafiya Jari ya ji ta bakin wasu mata, da ma illolin hakan ga lafiyar uwa da jariri.
A Najeriya mata masu sana'ar finafinan Hausa na fuskantar kalubalai da dama ciki har da zargin gurbata tarbiyar jama'a.
Shirin ya yi nazari dangane da matsalar Bleaching a tsakanin matasa maza da mata domin fatarsu tai haske.
A yankin arewacin Najeriya, inda ake bai wa asali da addini muhimanci, masu sharhi kan zamantakewar na ganin akwai bukatar jama'ar yankin su yi karatun ta natsu wajen kula da yadda suke amfani da shafukan sada zumunta don kare kimar addini da al’ada.
Aishatu Kabu Damboa 'yar gwagwarmaya ce kan samar da daidaito a tsakanin jinsi, a Maiduguri babban birnin jihar Borno a yankin Arewa maso Gabashin Najeriya.
Najeriya na daga cikin kasashen da iyaye ke ba wa yara 'yan mata manyan wayoyi a matsayin gata ba tare da la'akari da yadda hakan ke gurbata tarbiyar kanana yaran ba.
Mata kan bata lokaci mai yawa wajen yin kwaliyya, kasancewa yin kwalliyar na zaman abin birgewa musamman ga matan. Shin ko hakan na da wata illa ga lafiyar jiki mussaman wa fata?