Muna amfani da "Cookies" domin inganta abubuwan da muke wallafawa a intanet. Za ku iya samun karin bayani a kundin kare bayananmu.
Hukumar hana ta'ammali da kwayoyin kara kuzari a wasanni wada, ta haramtawa Rasha shiga harkokin wasanni na tsawon shekaru hudu.
Bayan kun saurari labarai, za ku ji rahoton Hukumar Lafiya ta Duniya WHO game da yawaitar magunguna marassa inganci a kasashe masu raunin tattalin arziki.
A cikin shirin za ku ji yadda a Najeriya ta leko ta koma ga madugun kiran juyin juya hali Omoyele Sowere, sa'oi kalilan da sakinsa jami’an hukumar tsaro na farin kaya sun sake kame shi a lokacin da ya bayyana a babban kotun Abuja.
Cikin shirin za a ji martani daga Najeriya kan aika shugaban 'yan Shi'a gidan yari da kotu ta yi a wannan Alhamis. Akwai ma batun sarkakiyar tsaro a yankin Sahel musamman kyamar da sojojin Faransa ke fuskanta.
A cikin shirin bayan an saurari labaran duniya za a ji cewa wata kotu a Kadunan Najeriya ta yanke hukuncin sake mayar da jagoran mabiya mazhabar Shi'a Ibrahim El-zakzaky da mai dakinsa a gidan yari.
A cikin shirin muna tafe da rahoto kan yadda gwamnat ta haramta amfani da babura masu kafa uku wato Keke Napep ko kuma adaidata sahu a manyan titunan jihar Borno.
Zanga-zanga a daidai lokacin da ake taron kasashen duniya a Spain kan batun muhalli don kammala dokokin fara aiki da yarjejeniyar Paris ta 2015.
Nazari kan mu'amula da ke tsakanin ma'autara da ke aiki suna samun albashi.
A cikin shirin muna tafe da karin bayani kan halin da ake ciki a gasar Bundesliga ta Jamus da La Liga da Premier League da Nigerian Premier League da sauran wasanni.
Bayan labarun duniya muna dauke da rahoto game da zagayowar ranar da Majalisar Dinkin Duniya ta ware don wayar da kan al'umma game cuta mai karya garkuwar jiki.
Jami'an 'yan sandan Birtaniya sun bayyana mutumin da ya kashe mutane biyu ta hanyar caka musu wuka a kan babbar gadar birnin London, da zama wani tsohon fursuna, da ya yi zaman gidan maza bisa laifukan ta'addanci, kafin a sakeshi bara
Za kuji cewar hukumar kula da al'adu ta Majalisar Dinkin Duniya UNESCO, ta sanya birnin Babilon na kasar Iraki cikin jerin wuraren tarihi masu daraja a duniya.
A cikin shiri bayan labaru duniya akwai rahotanni kamar haka: Kungiyoyin farar hula da masu rajin kare dimukurdiyya a najeriya sun gudanar da zanga-zangar lumana a Abuja don nuna adawarsu da kudurin doka kan hukunta masu furta kalaman batanci, al'ummar jihar Damagaram sun ce ba sa cin gajiyar matatar mai da aka girka a kasar ta Nijar shekaru 8 da suka gabata.
A cigaba da martani kan matakin majalisar dottawan Najeriya, Majalisar Dinkin Duniya ta nuna rashin dacewar hukuncin kisa da aka tanadar wa masu laifin yin kalaman batanci ta yanar gizo
Shirin na kunshe da rahotanni da labaran duniya daga sassan dabam-dabam, ciki har da yadda Majalisar Dinkin Duniya ta yaba da matakin da gwamnatin Jamus ke dauka don ganin ta kare muhalli daga illolin da Sauyin yanayi ke haifarwa.
Shirin ya kunshi labaran duniya da rahotanni ciki kuwa har da shirin da babbar jam'iyyar adawa ta Jamhuriyar Kamaru ta yi na kauracewa zabukan 'yan majalisa da na shugabannin kananan hukumomi.
Babbar jam'iyyar adawa ta MRC a Kamaru ta sanar da cewa ba za ta shiga a zabukan da kasar za ta shirya a shekara ta 2020 ba, sabili da rashin tsaro a yankunan masu magana da Turancin Inglishi.
Matakin gwamnatin Chadi na shirin aikawa da sojojin kasar a wasu kasashen Sahel domin yaki da kungiyoyin 'yan ta'adda ya haifar da zazzafar muhawara a kasar ta Chadi kan dacewar matakin.
Auren wuri na yara ya bazu a Najeriya. 'Yan matan ana yi musu aure saboda dalilai na al'adu da talauci kuma dokar tsarin mulkin Najriya ba ta haramta auren wuri ba amma wasu matan na yin fafutuka domin samun sauyi.