Muna amfani da "Cookies" domin inganta abubuwan da muke wallafawa a intanet. Za ku iya samun karin bayani a kundin kare bayananmu.
Masu zanga zangar sun cinn wuta a katafaren ginin sayer da kayayyaki na Shoprite da ke unguwar gidajen Jakande bayan sun kona babbar kotun kasa da ke unguwar Abosere, a birnin na Legas cibiyar kasuwancin Najeriya.
Bayan labaran duniya akwai rahotanni kan halin da ake ciki a Najeriya, inda gwamnatin jihar Legas ta ce za ta kaddamar da bincike a game da zargin mutuwar masu zanga- zanga a sakamakon bude musu wuta da aka ce sojoji sun yi a jiya Talata.
Mai sana'ar daukar hotuna 'dan Najeriya, mazaunin Jamus tsahon shekaru 50, da ya kan zagaya kasashen duniya domin daukar hotuna iri-iri a birane da wajen gari. An baje ayyukansa a filin bajekolin hotuna na birnin Berlin
Bude filayen jiragen sama na Abuja da Legas a Najeriya bayan kwashe fiye da watanni uku da rufe su sakamkon cutar sarkewar numfashi ta Covid 19.
A cikin shirin akwai rahoto a kan sasanci a tsakanin makiyaya da manoma a Adamawan Najeriya da rahoto a kan sufurin jirgin ruwa a Legas da kuma rahoto a kan bikin al'ada da ake kira 'Yenandi' a Gaya Jamhuriyar Nijar da rahoto a kan kasuwanci da wayar salula a Kamaru.
A cikin shirin za a ji cewa gwamnatin Najeriya ta bayar da umarnin yin sakin mara ga dokar kulle da take dauka a wasu jihohin kasar masu fama da annobar coron ciki har da jihar Legas, to amma bisa sharadin cika wasu ka'iddodin da gwamnatocin jihohin za su gindaya. A Jamhuriyar Nijar wata takaddama ce ta barke tsakanin dalibai da gwamnati.
Hukumomi a Najeriya sun yi barazanar sake kulle babban birnin kasar na Abuja da kuma jihohin Legas da Ogun.
A cikin shirin za a ji cewa adadin wadanda suka kamu da cutar corona a yanzu sun haura miliyan biyu a yayin da dubu 147 daga cikinsu suka rigamu gidan gaskiya, kana kuma za a ji cewa wasu hotunan jabu ne suka karade jihohin Legas da Ogun kan jita-jitar cewa 'yan kungiyar One million Boys na shirin kaddamar da hare-kare kan al'umma.
A cikin shirin za ku ji cewa sanadiyar fashewar bututun mai a jihar Legas an sami asarar rayukan mutane da dama kana kuma akwai shirin Ra'ayin Malamai na musamman.
Shirin na kunshe da labaran duniya. Za a ji matakan da ake dauke kan dakile yaduwar Covid-19 a Legas. Sai batun karbar cin hanci daga wajen masu neman ayyuka a Najeriya da ya zama kalubale ga 'ya'yan marasa galihu.
Nazari kan nasarori da matsaloli ko kuma kalubale da mata ke fuskanta a yayin da suke amfani da kafafen sada zumunta na zamani. Mata na iya tallata hajojinsu a kafafen sada zumuntar na zamani, sai dai kuma wasu matan kan fuskanci cin zarafi.
A cikin shirin za ku ji cewar ta tabbata an sami wannan cutar ta Coronavirus a jihar Legas a jikin wani dan kasar Italiya wanda ya shiga Kasar.
A cikin shirin za a ji cewa, cutar Coronavirus ta bulla a jihar Legas da ke tarayyar Najeriya dama wasu karin rahotanni da labarai daga sassan duniya.
Saboda tasirin shafukan sada zumunta ne musamman tsakanin matasa, shirin ya karkata akalarsa kan makon shafukan sadarwar da aka bude a birnin Legas da ke kudancin Najeriya.
Shirin ya kunshi labaran duniya da halin da 'yan arewacin Najeriya masu sana'o'i ke ciki a Legas inda hukumomi ke bijiro da sabbin dokoki. Akwai ma halin da ake ciki a Jamus bayan hare-haren wasu kyamar baki a birnin Hanau.
Bayan kun saurari Labarai muna tafe da rahoton bikin al'adun gargajiya na Carnival a birnin Bonn da ke tarayyar Jamus, sai kuma rahotonmu na musamman daga jihar Legas Najeriya.
Bayan kun saurari Labarai, muna tafe da rahoton yadda dubban matasa masu sana'ar Achaba suka koma garin Dutse jihar Jigawa a Najeriya sakamakon haramta sana'ar kabu-kabu a jihar Legas.
Cikin shirin za a ji yanda matasa a Nijar suka kama shiga aikin soji da na dan sanda, bayan fahimtar da suka yi cewar nasarar kasa sai dai sadaukarwa. A Najeriya har yanzu an gaza kai karshen shari'ar da ake yi wa wasu da aka zarga da neman jinsi a Legas. Chadi ta bai wa baki 'yancin zabe.
Haramta amfani da ababen hawan ya biyo bayan hadura da cunkoso da gwamnatin jihar Legas ta ce suke haifarawa, dole ta dauki matakin duk da suka da ta ke ci gaba da sha daga masu sana'ar da wadanda ke dogaro da ababen hawan a zirga-zirga.
Unguwar talakawa ta Makoko da ke cikin ruwa a jihar Legas da ke Najeriya, ba ta cikin kundin bayanan tsare-tsare na birnin. Sai dai yanzu ana kokarin kawo sauyi don saka Makoko mai yawan mutane 300,000 a taswira.