Muna amfani da "Cookies" domin inganta abubuwan da muke wallafawa a intanet. Za ku iya samun karin bayani a kundin kare bayananmu.
A cikin shirin bayan labaran duniya za ku ji yadda Shugaba Joe Biden na Amirka ya sha rantsuwar kama aiki. Muna dauke da rahoto game da martanin da ’yan Najeriya da Nijar da sauran kasashen Afirka ke yi game da kama aikin da Joe Biden ya yi.
A cikin shirin za a ji cewa dakarun tsaron Najeriya sun kwace iko da barikin sojan garin Marte da ke yankin Arewa maso gabashin Najeriya, a yayin da sojan Munisca naMajalisar dinkin Duniya a Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya suka karbe iko da garin Bagassou daga hannun 'yan tawaye.
A cikin shirin za a ji cewa Bayan fafatawa tsakanin 'yan takara, gwamnan jihar NRW Armin Laschet, ya yi nasara a zaben shugabancin jam'iyyar CDU. Akwai shirin ciniki da masana'antu da amsosshin takardunku da shirin wasikun masu saurare da kuma Kloba.
Dakarun gwamnati a Jamhuiryar Afirka ta Tsakiya sun sanar da dakile 'yan tawayen da suka yi kokarin karbe iko da babban birnin kasar Bangui.
Gwamnatin Jamus na biyan kudi ga ofisoshin jakadanci kasashen ketare domin tantance 'yan aksarsu da ke zaune ba tare da izini ba.
Tsawaita tarnaki na matakan Corona da Jamus ta yi na kara tsaurara halin rayuwar yara 'yan makaranta da iyayensu.
A cikin shirin za a ji cewa jam'iyyun adawa a Nijar na neman samun goyon bayan 'yan siyasa don lashe zabe, a yayin da a Amirka Shugaba Donald Trump da mataimakinsa Mike Pence suka yi alawashin ci gaba da mulki tare duk da kalubalan da suke fuskanta daga 'yan jam'iyyar Demokrat.
A cikin shirin bayan labaran duniya akwai rahoto kan sabon yunkurin majalisar dokokin Amirka na tsige shugaba Donald Trump daga kujerar mulki da rahoto kan martanin da ake yi a kasar Yemen bayan Amirka ta sanya kungiyar Houthi cikin jerin kungiyoyin ‘yan ta’adda na duniya da rahoto kan rudanin da ke tattare da sake bude jami’o’in Najeriya saboda sabon rikicin da ya dabaibaye jami’o’in gwamnati.
A cikin shirin za a ji yadda 'yan a ware na Ambazoniya su ka zafafa kai hare-haren mai kan uwa da wabi.
A cikin shirin bayan labaran duniya akwai rahoto kan kubuto mutane sama da 100 a jihar Katsina da rahoto kan yadda wasu 'yan takara a Nijar suka tafi kotu game da yadda aka gudanar da zaben da ya gabata da sharhunan jaridun Jamus.
A cikin shirin za a ji cewa Duniya na ci gaba da caccakar shugaban Amirka Donald Trump, a yayin da aka kakaba dokar hana fitar dare a Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya bisa matsin lambar kungiyoyin yan tawaye.
Za a ji kasashen yamma ciki har da Jamus na kira ga Sin da ta gaggauta sakin 'yan adawa 50 da aka kame a Hong Kong.
A cikin shirin a Tarayyar Najeriya, batun karba-karba ne ya fara daukar hankullan 'yan kasar, kusan shekaru biyu gabanin komawa runfunan zabe.
Za a ji yadda kungiyoyi ke martanin kisan mutane 100 da 'yan bindiga suka yi a Nijar
A cikin shirin za a ji cewa Sojojin Aljeriya sun hallaka a yayin wani taho mu gama da 'yan ta'adda, akwai shirin Ji Ka Karu da shirin Darasin Rayuwa da Rayin Malumai.
A cikin shirin za a ji shugaban Najeriya Mohammadu Buhari ya rattaba hannu kan sabon kasafin kudi da ya ke sa ran amfani da shi wurin kawar da matsalar tsaro da ginawa 'yan kasar sabuwar rayuwa.