MDD: Tuni da ranar ayyukan jinkai ta duniya
August 19, 2024Ma'aikatan agaji da dama sun rasa rayukansu a fagen daga a 2023 fiye da kowace shekara a baya a cewar ofishin Majalisar Dinkin Duniya mai kula da ayyukan jin kai OCHA.
Ma'ikatan agaji 280 suka rasa rayukansu a bara, adadin da hukumar ta OCHA ta ce ya yi muni matuka.
A cikin wata sanarwa mai dauke da alkaluman wanda aka wallafa a wannan Litinin, ranar tuni da ayyukan agaji a duniya, shugabar riko ta OCHA Joyce Msuya ta ce ana amfani da kisa domin hana aiwatar da adalci ga wadanda da aka ci zalunta domin samar da yanayin da masu wannan ta'asa za su ci gaba da aikata danyen aikinsu.
Wuraren da aka samu hasarar ma'aikatan agaji da yawa sun hada da Gaza da Sudan da Kudu da kuma Sudan. Sauran sun hada da Ukraine da Rasha da yankin Amhara na kasar Habasha da kuma Syria. Sai Somalia da Myanmar da Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango