1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

MDD: Talauci ne tushen tsattsauran akida

September 10, 2017

Bincike da Majalisar Dinkin Duniya ta gudanar kan tushen tsattsauran akida a tsakanin matasa a Afirka ya gano yana da alaka da talauci da rashin shugabanci na gari

https://p.dw.com/p/2jf0O
Somalia Al-Shabaab Kämpfer
Hoto: picture alliance/AP Photo/M. Sheikh Nor

A wani rahoto da ta fitar kan tushen tsattsauran akida a tsakanin matasa a Afirka, Majalisar Dinkin Duniya ta danganta lamarin da talauci da rashin shugabanci na gari.

Rahoton ya ce matsanancin talauci da mayar da wasu saniyar ware da kuma rashin kyakkyawar shugabanci sun fi taka rawa wajen sanya matasa zama masu tsattsauran akida sabanin addini.

Majalisar Dinkin Duniyar ta cimma wannan matsaya ne bayan da ta tattauna da mutane kimanin kusan 500 tsoffin yan kungiyoyin tarzoma kamar Boko Haram a Najeriya da al Shabaab a Somaliya da kuma tsoffin yan kungiyar IS a Sudan.

A bisa alkaluman kididdiga na hukumar raya cigaba ta Majalisar Dinkin Duniya UNDP mutane fiye da dubu 33 aka hallaka a sakamakon hare-hare masu nasaba da tsattsauran akida a Afirka a shekarar 2011 da kuma farkon shekarar 2016.

Rahoton ya ce kungiyar Boko Hara kadai ta yi sanadiyar mutuwar mutane kimanin dubu 17 tare da sanya wasu fiye da miliyan biyu da dubu dari takwas yin kaura daga matsugunansu da kuma haddasa tagaiyarar al'umma a yankin tafkin Chadi.