MDD ta yi shelar neman agajin kudi | Labarai | DW | 07.12.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

MDD ta yi shelar neman agajin kudi

Majalisar Dinkin Duniya ta yi shelar neman agajin kudi sama da biliyan 20 na dalar Amirka ga kasashe mambobinta domin taimaka wa mutane miliyon 87 a kasashe 37 na duniya a shekara ta 2016.

Majalisar Dinkin Duniya ta yi shelar neman agajin kudi sama da biliyan 20 na dalar Amirka ga kasashen mambobinta domin taimaka wa mutane miliyon 87 a kasashe 37 na duniya a shekara ta 2016.

Stephen O'Brien Mataimakin babban magatakardan Majalisar Dinkin Duniya kana jagoran sashen kula da ayyukan jin kai da kawo daukin gaggawa na hukumar wanda ya sanya wannan kira a wannan Litanin, ya ce wannan shi ne neman agaji mafi girma da Majalisar Dinkin Duniya ta taba yi a cikin shekaru 10 na baya bayan nan.

Kuma ya ce suna bukatar taimakon ne domin fiskantar abin da ya kira kalubalen rayuwa mafi girma da duniya ba ta taba gani ba a shekaru 30 na baya-bayan nan da ke da nasaba da yake-yaken da ake fiskanta a kasashen Siriya iraki Sudan ta Kudu da Yemen wadanda suka saka miliyoyin mutane maza da mata musamman kananan yara cikin gudun hijira da halin rayuwar kunci.