1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

MDD ta yi gargadi game da ruruwar rikici a gabashin Kwango

Mouhamadou Awal Balarabe
July 10, 2024

Manzon musamman na Majalisar Dinkin Duniya a Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango Bintou Keita ta bayyana cewa akwai barazanar yaduwar yaki da ake yi a gabashin kasar tsakanin dakarun gwamnati da 'yan tawayen M23.

https://p.dw.com/p/4i73c
Bintou Keita a zauren Majalisar Dinkin Duniya a New York
Bintou Keita a zauren Majalisar Dinkin Duniya a New YorkHoto: Li Muzi/Xinhua News Agency/picture alliance

 A cikin rahotonta da ta gabatar a gaban kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya, Bintu Keita ta nunar da cewar kasashen Ruwanda da Yuganda na dada angiza wutar rikic a gabashin Kwango tsakanin dakartun gwamnati da 'yan tawayen M23, lamarin da ke haddasa fargaba a a yankin Ituri.

Keita ta ce: "Matsalar tsaro a gabashin Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango na ci gaba da tabarbarewa, abin da ke ta'azza tashin hankali da haifar da gudun hijira na mazauna yankin. Na yi matukar kaduwa game da yaduwar kungiyar M23 a arewacin Kivu da kudancin yankin, da hare-haren da ake kaiwa kan cibiyoyin gwamnati wadanda ke samun goyon bayan Majalisar Dinkin Duniya:"

Sai dai rundunar sojin Yuganda ta nemi wanke kanta inda ta ce zargin marar hannu a rikicin Kwango ba shi da tushe da makama. Hakazalika, Majalisar Dinkin Duniya ta kara da cewa Ruwanda na ci gaba da goyon bayan 'yan tawayen M23.