1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An kasa samun matsaya kan zaben Libiya

Abdul-raheem Hassan
June 30, 2022

Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana cewa tattaunawar da aka yi tsakanin hukumomin Libiya da masu adawa da juna kan ka’idojin zaben da aka dade ana jira ta gaza cimma matsaya kan wasu muhimman bambance-bambance.

https://p.dw.com/p/4DURD
Tattaunawar sulhu kan Libiya a birnin GenevaHoto: UNITED NATIONS/AFP

Kakakin majalisar dokokin kasar Aguila Saleh da shugaban majalisar kolin kasar Khaled Al-Mishri sun gana a birnin Geneva na tsawon kwanaki uku, domin tattaunawa kan daftarin tsarin mulki da dokar zabe.

Sai dai duk da wasu ci gaba da aka samu, bai isa a ci gaba da shirin manyan zabukan kasar ba, kasancewar har yanzu bangarorin biyu suna takun saka kan wanda zai iya tsayawa takara a zaben shugaban kasa, in ji babbar jakadar MDD a Libya, Stephanie Williams, wacce ta jagoranci tattaunawar.

Zaben shugaban kasa da na 'yan majalisar dokokin kasar da aka shirya yi a watan Disambar bara, na da nufin gudanar da shirin zaman lafiya karkashin jagorancin Majalisar Dinkin Duniya bayan kawo karshen rikicin da ya barke a shekarar 2020.

Sai dai ba a taba kada kuri'ar ba, saboda wasu ‘yan takara masu cike da cece-kuce da kuma rashin jituwa mai zurfi, dangane da ka'idojin zabe, tsakanin cibiyoyin samar da wutar lantarki a gabashi da yammacin kasar.