MDD ta gargadi sabon shugaban Burundi | Labarai | DW | 14.07.2020
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

MDD ta gargadi sabon shugaban Burundi

Majalisar Dinkin Duniya ta yi kira ga sabuwar gwamnati Burundi da ta kawo karshen tashin hankalin da ake fama da shi a kasar.

A cikin wata sanarwa da kwamitin bincike na MDD a kan Burundi ya bayyana ya bukaci sabon shugaban na Burundi Évariste Ndayishimiye ba da hadin kai wajen sake bude cibiyar kare hakin dan Adam ta majalisar a Burundi.Tun a shekara ta 2016 kwamitin kare hakin dan Adam na MDD ya soma gudanar da bincike a kan tafka ta'asa a Burundin. Tashin hankali biyo bayan zaben da aka yi a shekara ta 2015 mutane dubu 12 suka mutu, yayin da wasu dubu 400 suka yi kaura daga kasar.