1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

MDD ta dage wa Eritriya takunkumi

Gazali Abdou Tasawa
November 14, 2018

Majalisar Dinkin Duniya ta dage wa Eritriya jerin takunkuman da ta saka mata a sakamakon mamaye wani yankin kasar Djibouti shekaru 10 da suka gabata da ma zargin tallafa wa kungiyoyin 'yan ta'adda. 

https://p.dw.com/p/38GaH
UN-Sicherheitsrat in New York | Debatte Sanktionen gegen Eritrea
Hoto: picture-alliance/Xinhua News Agency/L. Muzi

Illahirin kasashe mambobin kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya suka amince da dage wa kasar ta Eritriya jerin takunkuman a sakamakon yarjejeniyar zaman lafiyar mai cike da tarihi da ta cimma da kasar Habasha da ma kuma kyautata dangantakarta da kasar ta Djibouti. 

Kudirin Majalisar Dinkin Duniya ya kuma kira ga kasashen Eritriya da Djibouti da su ci gaba da kokarin shawo kan rikicin da ya hada su, kana ya yi kira ga mahukuntan Asamara da su bayar da bayanai kan makomar sojojin kasar Djibouti da suka bata bayan yakin da kasashen biyu suka gobza shekaru 10 da suka gabata. 

A shekara ta 2009 ne dai Majalisar Dinkin Duniya ta saka wa kasar ta Eritriya takunkumin hana sayar mata da makamai da haramta wa shugabanninta tafiye-tafiye da ma kame kudaden ajiyarsu an banki a bisa zargin ta da tallafa wa kungiyoyin masu da'awar jihadi na kasar Somaliya.