MDD: Ta ce kisan Rohingyas da gangan ne. | Labarai | DW | 11.10.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

MDD: Ta ce kisan Rohingyas da gangan ne.

Sakamakon wani bincike da kwararru na MDD suka kaddamar ya nuna cewar kisan da aka rika yi wa 'yan kabilar Rohingyas na kasar Bama da gangan ne.

Rahoton na Majalisar Dinkin Duniya ya ce kisan wani abu ne da aka tsara da nufin kawar da tsirarun kabilun Musulmi na Rohingyas baki daya daga kasar ta Bama. Masu yin binciken sun yi tambayoyi ga gomai na jama'ar da suka tsere daga yankin Rakhine zuwa Bangladesh bayan barkewar tashin hankalin a cikin watan Augustan da  ya gabata