MDD ta ce ana ci gaba da yi wa ′yan Yesidi kisan gilla | Labarai | DW | 03.08.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

MDD ta ce ana ci gaba da yi wa 'yan Yesidi kisan gilla

Majalisar Dinkin Duniya ta yi nuni da binciken da ta yi da ya nuna har yanzu akwai mata da yara sama da 3200 na 'yan Yesidi a hannun 'yan takifen na kungiyar IS.

Shekaru biyu bayan kisan gillan da mayakan kungiyar IS suka yi wa 'yan Yesidi a arewacin Iraki, Majalisar Dinkin Duniya ta ce har yanzu ana matukar cin zarafin tsirarun mabiya addinin a Siriya. A lokacin da take ba da sanarwa yayin zagayowar shekaru biyu da farmakin da mayakan IS suka kai a yankin 'yan Yesidi a ranar 3 ga watan Agustan shekarar 2014, hukumar kare hakkin dan Adam ta Majalisar Dinkin Duniya ta yi nuni da binciken da ta yi da ya nuna har yanzu akwai mata da yara sama da 3200 na 'yan Yesidi a hannun 'yan takifen na kungiyar IS. Ta ce an mayar da mata da 'yan mata tamkar bayi ana kuma lalata da su, yayin da samari matasa kuma ake cusa musu munanan akidoji ana kuma horas da su aikin soji.