MDD ta bukaci bincike kan kisan fararan hula a Bama | Labarai | DW | 25.10.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

MDD ta bukaci bincike kan kisan fararan hula a Bama

Majalisar Dinkin Duniya ta bukaci gwamnatin kasar Bama ko Myanmar da ta gudanar da bincike kan al'amarin kisan farararn hula da sojoji suka yi da ma kone wasu kauyika a Yammacin kasar a makonnin baya bayan nan

Majalisar Dinkin Duniya ta bukaci gwamnatin kasar Bama ko Myanmar da ta gudanar da bincike kan al'amarin kisan farararn hula da sojoji suka yi da ma kone wasu kauyika a Yammacin kasar a makonnin baya bayan nan. Lamarin da ya tilasta wa dubunnan mutane tserewa daga garuruwansu domin tsira da rayukansu.

Majalisar Dinkin Duniyar ta bayyana wannan matsayi nata ne a cikin wata sanarwa da ta fitar a Yammacin jiya Litinin inda ta ce gwamnatin kasar ta Bama ba ta da hujjar kisan mutane a bisa zargi kawai na aikata wani babban laifi. 

A farkon wata Oktoban nan ne dai bayan wani hari da aka kai kan wani ofishin 'yan sanda, gwamnatin kasar ta Bama ta tura sojoji a yankin inda suka yi ta kisan musulmai 'yan kabilar Rohingyas a bisa zargin cewa daruruwan daga cikinsu da suka samu horo daga Kungiyar Taliban ke da alhakin kai wannan hari.