MDD: Shirin yakar ta′addanci a Mali da Burkina | Labarai | DW | 22.03.2019
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

MDD: Shirin yakar ta'addanci a Mali da Burkina

Tawagar kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya ta isa kasar Mali da burin shawo kan matsalar ta'addanci da ta addabi kasar da kuma Burkina Faso, inda za ta kuma duba yadda za a karfafa kungiyar G5 Sahel.

Baya ga Mali, an shirya bai wa gwamnatin Burkina Faso cikakken goyon baya a yunkurin da take na yakar ayyukan masu tayar da kayar baya. Jakadan kasar Afirka ta Kudu a Majalisar Dinkin Duniya Jerry Matjila da ke cikin tawagar, ya ce burinsu, shi ne a kawar da barazanar da ayyukan ta'addanci ke yi ga rayuwar al'umma.

Ya baiyana damuwa kan irin tsekon da suke fuskanta, sai dai ya ce ya zama dole a dauki mataki. Tawagar ta fara isa birnin Bamako na kasar Mali inda za ta kwashi kwanaki biyu tana tattaunawa kan batun tsaron  kafin ta karkare ziyarar a birnin Ouagadougou na kasar Burkina Faso..