MDD: Mutane na fama da matsala a Yemen | Labarai | DW | 10.05.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

MDD: Mutane na fama da matsala a Yemen

Majalisar Dinkin Duniya ta ce bisa ga dukkan alamu mutum dubu 500 na iya shiga mawuyacin hali a yankin Arewa maso yammacin kasar Yemen muddin aka gaza daukar matakai cikin hanzari.

Kakakin hukumar kula da 'yan gudun hijira ta MDD a lardin Taez na Yemen Shabiya Mantoo, ya ce daruruwan mutane ne suka rasa muhallinsu kuma ke fama da karancin abinci, duk da cewa rikici bai kazanta ba a kasar, kuma galibinsu a yankin Hudeida ne.

A cewar jami'in a halin da ake ciki akwai mata da kananan yara masu yawa da ke barar abin da za su ci a manyan tituna, sakamakon yawan jama'ar da ta yiwo hijira shekaru biyun da suka gabata.

Akalla rayuka mutam dubu 7 da 700 ne suka salwanta yayin da wasu miliyoyi suka rasa muhalli, sakamakon rikici a Yemen a shekara ta 2015.