1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Majalisar Dinkin Duniya ta yi na'am da shelar 'yan Huthis

Abdoulaye Mamane Amadou
September 22, 2019

Majalisar Dinkin Duniya ta jinjinawa matakin kungiyar Houthis na dakatar da kai hare-hare a Saudiyya, tare da cewa matakin kan iya kara bude wata kafa ta kawo karshen yakin basasar da Yemen ta fantsama a ciki.

https://p.dw.com/p/3Q1zg
Jemen Hafenstadt Hudaida ARCHIV
Hoto: picture-alliance/dpa/H. Al-Ansi

A cikin wata sanarwar da Majalisar Dinkin Duniya ta wallafa ta bukaci 'yan tawayen Houthis da su tabbatar da wata yarjejeniyar tsagaita wuta da aka cimma a watan Disamba, musamman batun musanyar fursunonin yaki, tana mai cewa hanyar siyasa ce kawai za ta iya kawo karshen yakin da ya daidaita kasar ta Yemen.

Sai dai da take mayar da martani game da marakin kungiyar ta 'yan tawayen Houthis, kasar Saudiyya ta ce ba za ta iya tabbatar matakin ba kawai a baki face sai ta gani a zahiri.