1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaJamus

MDD za ta kwashe iyalan ma'aikatanta a Habasha

Abdoulaye Mamane Amadou
November 23, 2021

Ana shirin kwashe iyalan ma'aikatan Majalisar Dinkin Duniya da ke aiki a Habasha a yayin da rikici tsakanin 'yan awaren Tigrey da gwamnatin tarayya ke kara ta'azzara.

https://p.dw.com/p/43Nxr
Äthiopien Premierminister Abiy Ahmed stellt im Parlament sein neues Kabinett vor
Hoto: Ethiopian Prime Minister Office

Majalisar Dinkin Duniya za ta kwashe iyalan ma'aikatanta da ke aiki a Habasha nan da zuwa ranar 25 ga wannan wata na Nuwamba.

Ita ma dai kasar Faransa ta bi sahun Birtaniya a wannan Talata, inda ta yi kira ga 'yan kasarta da su gaggauta ficewa daga Habasha, duba da yadda rikici ke kara tsananta a cewar wata wasikar da ofishin jakadancin kasar ya fitar.

Tun farko sakataren harkokin wajen Amirka Antony Blinken, ya yi fargabar kara dagulewar al'amura a Habasha, muddin ba a sulhunta rikicin da ya barke ba tsakanin 'yan awaren Tigrey da gwamnatin tarayya mai shalkwata a birnin Addis.

Wata majiyar diflomasiyar da bata so a ambaci sunanta ba, ta shaida wa kamfanin dillancin labarai na AFP cewa ana gwabza fada a yankin Debre Sina mai tazarar kilomita 30 daga babban birnin kasar Habasha tsakani 'yan awaren TPLF da dakarun gwamnati.