MDD ka iya tura dakaru a yankin kan iyaka tsakanin Chadi da Sudan | Labarai | DW | 28.10.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

MDD ka iya tura dakaru a yankin kan iyaka tsakanin Chadi da Sudan

Dan Halutz

Dan Halutz

A dangane da bazuwar rikicin lardin Darfur na yammacin Sudan, MDD na duba yiwuwar fadada aikin zaman lafiyar ta zuwa kasar Chadi makwabciyar Sudan. Wakilin MDD a yankin Jean-Marie Guehenno ya ce ana iya mikawa kwamitin sulhun MDD batun na girke wata tawagar sa ido ko ma dakarun wanzar da zaman lafiya a yankin kan iyakar Chadi da Sudan. A yau dai gwamnatin Chadi ta zargi mayakan sama na Sudan da kai hare hare kan wasu kauyukanta 4 dake kan iyakarta da lardin Darfur. To sai dai babu labari game da rayukan da suka salwanta sakamakon hare haren. Sudan da Chadi dai na zargin juna da goyawa ´yan tawayen kasashen biyu baya.