MDD: Jan kunne kan cin zarafi a Kwango | Labarai | DW | 14.11.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

MDD: Jan kunne kan cin zarafi a Kwango

Majalisar Dinkin Duniya ta yi hannunka mai sanda ga hukumomin kasar Kwango kan duk wani mataki na cin zarafin jama'a yayin babbar zanga-zangar da 'yan adawa suka kira ta ranar Laraba 15 ga watan Nuwamba.

'Yan adawan kasar ta Kwango dai sun kira zanga-zangar ce a ranar Labara 15 ga watan nan na Nuwamba a fadin kasar domin nuna adawarsu ga sabon jaddawalin zabukan kasar da aka fitar, wanda kuma ya kara wa'adin zaman shugaba Joseph Kabila a kan karagar mulki har ya zuwa watan Janairu na 2019.

Dangane da nauyin da ya rataya a kanshi na rashin tsoma baki a cikin lamurra na kasar ta Kwango, ofishin Majalisar Dinkin Duniya a kasar ta Kwango na MONUSCO ya ce zai bi lamarin sau da kafa, kuma zai sanar da duk wani yanayi na cin zarafi bil-Adama a cewar Maman Sidikou babban wakilin Majalisar Dinkin Duniya a kasar ta Kwango, inda ya yi kira ga hukumomin da su yi  biyayya ga hakkokin jama'a musamman ma kan incin yin taruka, ko zanga-zanga dai dai yadda kundin tsarin mulkin kasar ya tanada.

Sau tari jami'an tsaro a kasar ta Kwango kan cin zarafin masu zanga-zanga, kaman yadda ya gudana yau da wata guda a birnin Goma da ke gabashin kasar, inda hakan ya yi sanadiyyar mutuwar mutane da dama.