MDD: Fara raba abinci a garuruwan Siriya | Labarai | DW | 17.02.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

MDD: Fara raba abinci a garuruwan Siriya

A wannan Larabarce Jakadun Majalisar Dunkin Duniya ke fara kai kayayyakin agaji a wasu garuruwa bakwai da yaki ya ritsa da su, kuma ke cikin mawuyacin hali na bukatu.

Yini guda bayan da Turkiyya ta sanar da kai hari a kan makwabciyarta da yaki ya daidaita, humumomin Majalisar Dunkin duniya na shirye ayarin motocin kai kayayyakin agajin gaggawa.

Gwamnatin Siriyar dai ta amince da a shigar da kayan agaji a cikin garuwa guda bakwai da aka yi wa kawanya, ciki har da Madaya, inda ake zaton mutane masu yawa sun rasa rayukansu sakamakon yunwa, kamar yadda matamakin mai magana da yawun babban sakataren MDD Farhan Haq ya nunar.

Ya ce "gwamnatin Siriya ta amince da a kai kayayyakin agaji a garuruwan da aka mamaye. A yanzu haka kungiyoyi da hukumomin agaji na shirya motocin da za su tafi wadannan yankuna cikin kwanaki masu gabatowa"

Da ya ke jawabi a birnin Damaskus, jakadan MDD Staffan de Mistura, ya ce a wannan Larabarce za'a fara raba kayan agajin, wanda zai kasance zakaran gwajin dafi na ko bangarori masu yaki da junan za su bari a taimakawa jama'a.