1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tashar nukiliya a Zaporizhzhia na cikin hadari

September 7, 2022

Hukumar makamashin nukiliya ta Majalisar Dinkin Duniya ta yi kiran samar da zaman lafiya da lumana a kusa da tashar nukiliya ta Zaporizhzhia wadda Rasha ta mamaye yayin da ake cigaba da luguden wuta a yankin.

https://p.dw.com/p/4GVaS
IAEO-Expertenmission besucht Kernkraftwerk Saporischschja
Hoto: Alexander Ermochenko/REUTERS

Sojojin Rasha sun kwace iko da tashar nukiliyar da ke zama mafi girma a nahiyar Turai.

A watan Maris an kai farmaki sau da dama kusa da tashar nukiliyar, lamarin da ya haifar da fargabar aukuwar mummunan bala'i na makamashin nukiliya.

Jm'ian hukumar makamashin nukiliya ta majalisar Dinkin Duniya IAEA sun ce halin da ake ciki yanzu a tashar nukiliyar bai dace ba.

Hukumar ta ce akwai bukatar gaggawa ta samar da wani shiri na wucin gadi domin kare aukuwar hadari a tashar nukiliyar.

A yayin taron Majalisar Dinkin Duniya Rasha ta ce abin takaici ne kwarai rahoton bai zargi Ukraine da kai hari kusa da tashar nukiliyar ba.