MDD ba zata tura tawagar zuwa Addis Ababa ba | Labarai | DW | 11.11.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

MDD ba zata tura tawagar zuwa Addis Ababa ba

Kwamitin sulhun MDD ta soke wani shiri da take yi na aikewa da wata tawagar zuwa Addis Ababa inda zata tattauna da jami´an gwamnatin Sudan da na kungiyar tarayyar Afirka AU game da rikicin lardin Darfur a ranar litinin. Jakadan Peru a MDD Jorge Voto Bernales wanda ke shugabantar kwamitin sulhun a yanzu ya ce sun kasa cimma matsaya daya a game da sakon da tawagar zata tafi da shi birnin na Addis Ababa. A karshen watan agusta kwamitin sulhu ya yanke shawarar tura dakaru dubu 2 zuwa Darfur don maye gurbin sojojin kiyaye zaman lafiya Afirka a yankin wadanda suka kasa hana zubar da jini. To amma gwamnatin Sudan ta nuna adawa da wannan shiri na girke sojojin MDD.