Mazauna karkara sun yi hannun ka mai sanda ga ′yan siyasa | Siyasa | DW | 06.02.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Mazauna karkara sun yi hannun ka mai sanda ga 'yan siyasa

A yayin da ya rage 'yan kwanaki a gudanar da zaben kasa a Tarayyar Najeriya al’umomin yankunan karkara sun yi tsokaci kan yadda 'yan siyasa ke ci da guminsu.

A duk lokacin da watan zabe ya tsaya a Najeriya 'yan siyasa da magoya bayansu kan fantsamzuwa cikin yankunan karkara domin yakin neman zabe. A wannan lokaci ne kuma ake yi wa al'umomin yankunan karkarar alkawura daban-daban da suka hada da na gina musu rijiyoyin burtsatse da makarantu da asibitoci da hanyoyin mota, banda uwa uba samar da takin zamani da ya zama turaren dan goma ga manoma a yankunan na karkara. To sai dai kuma akasarin wadannan alkawuran ana dauka ne ba tare da cikawa ba.

Nigeria - Landwirtschaft bei Katsina

Rashin Ilimi na taka rawa

To ko meyasa 'yan siyasar basa cika irin wadannan alkawuran da suke daukarwa talakawa. Alhaji Usman Musa kasuwar Garba tsohon dan siyasa ne kuma mai fashin bakin ka al'amuran siyasar a Najeriya, kuma a ganinsa baban abunda ke kawo haka shine akasarin mutanan karkara basu da ilimin zamani, domin idan aka yi musu alkawura, ko kuma suka gabatar da kokensu, a karshe sai wasu masu son zuciya su kewaye wannan dan siyasar su hana yai masa ayyuka domin ya kai ga cika wannan alkawarin da ya daukaka.

Ra'ayoyin mazauna Karkara

Amina Lawal freigesprochen

Malam Abubakar Dukku wani mazaunin karkara ne, kuma ya shaida cewar an dade ana ruwa kasa na shanyewa game da irin alkawuran da 'yan siyasa ke masu, sai dai tunda ance mai nema yana tare da samu ya gabatar da bukatunsa ga 'yan siyasar da suka hadar da asamar musu da hasken wutar lantarki da tsabtataccen ruwan sha da kuma hanyoyin zirga-zirga.

Sauti da bidiyo akan labarin