1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Mazauna Jarablus sun koma gida

Abdullahi Tanko BalaSeptember 7, 2016

A karon farko bayan 'yantar da garin Jarablus 'yan gudun hijirar sun fara komawa gida.

https://p.dw.com/p/1JxNm
Syrien Dscharabulus Amarne Selfie FSA Kämpfer
Hoto: Getty Images/AA/C. Ozdel

Wani ayarin yan Siriya su 292 sun koma gida Jarablus a yau Laraba a matakin farko na komawar fararen hula da suka yi kaura tun bayan da Turkiyya ta kaddamar da farmakin soji a yankin makonni biyu da suka wuce domin tabbatar da tsaron kan iyakarta, kamar yadda mahukuntan Turkiyyar suka baiyana.

Omar yana daya daga cikin yan gudun hijirar da suka koma garin.

"Cikin kyakyawar tarba mun koma kasarmu Siriya da kuma musamman garinmu jarablus. Mun gode wa Allah"

Garin jarablus dai wanda mayakan jihadi na IS suka kwace, shine na farko da sojin Turkiyya tare da hadin gwiwa da sojojin Siriya suka fara 'yantarwa bayan kaddamar da luguden wuta a garin a ranar 24 ga watan Agustan da ya gabata da nufin kakkabe mayakan jihadin.