Mazauna garin Damasak na cikin jimami | Labarai | DW | 24.03.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Mazauna garin Damasak na cikin jimami

Ba da dadewa ba ne dakarun Chadi da na Nijar suka 'yantar da garin Damasak amma kuma mazauna na zargin Boko Haram ta tafi da wasunsu

Mazauna garin Damasak da ke yankin Arewa maso gabashin Najeriya sun ce 'yan kungiyar Boko Haram sun kwashe 'yan mata da kananan yara fiye da 400 yayin da suke barin garin na su, wanda da ma dakarun Nijar da Chadi suka 'yantar a 'yan kwanakin baya-bayan nan.

Wani mai sayar da kayayyaki mai suna Suleiman Ali ya fadawa kamfanin dillancin labaran Reuters cewa a hasashenshi, mutanen da suka diba sun fi 500 kuma sun kashe kusan 50 daga cikinsu kafin suka wuce da wadanda suka rage, sai dai bayan sun bar wurin babu tabbacin ko sun kashe su ne, ko kuma sun tafi dukansu da yawansu haka.

Laftanant Kanar Toumaba Mohammed kwamandan rundunar sojojin Nijar da Chadi a Damasak ya ba da tabbacin cewa sun sami rahoton wannan sabon satar da kungiyar ta yi daga mazauna garin