Mayar da ′yan gudun hijira zuwa Turkiya | Labarai | DW | 04.04.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Mayar da 'yan gudun hijira zuwa Turkiya

A wannan Litinin din ce aka soma kwasar 'yan gudun hijira daga tsibirin Lesbos na Girka zuwa Turkiya a wani mataki na soma aiwatar da yarjejeniyar da aka cimma da Turkiya.

Duk kuwa da sukar da kungiyoyin kare hakin dan Adam ke yi wa lamarin, tuni dai da wannan safiya ta Litinin wasu manyan jiragen ruwan kasar Turkiya guda uku suka bar gabar ruwan tsibiran Lesbos da Chios na kasar Girka dauke da 'yan gudun hijirar zuwa kasar ta Turkiya.

Jirgin ruwan na farko dai ya dauki 'yan gudun hijira 131 wadanda akasarinsu 'yan kasashen Pakistan ne da kuma Bangladesh a cewar mai magana da yawun kungiyar Frontex mai kula da sa ido kan iyakokin waje na Tarayyar Turai. Wannan tsari dai ya shafi dukannin 'yan gudun hijirar da suka shiga kasar ta Girka ba bisa ka'ida ba wadanda yawansu ya kai a kalla mutun 6000.