Mayar da ′yan gudun hijira gida | Siyasa | DW | 16.03.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Mayar da 'yan gudun hijira gida

Mahukuntan Najeriya suna shirin mayar da 'yan gudun hijira na yankin arewa maso gabashin kasar zuwa gida wadanda rikici mai nasaba da Boko Haram ya shafa.

Wasu 'yan gudun hijira a jihar Adamawa ta Najeriya, na kiran mahukuntan kasar da su tabbatar da adalci gare su wajen samar da abubuwan bukata yayin da majalisar kasar ta ware masu kudade Naira bilyan goma domin tallafa masu komawa gidajensu.

Majalisar dattawa ta Najeriyar dai ta dauki wannan matakin ne tare da amannar cewa hankali ya kwanta a garuruwan da a baya suka kasance a hannun mayakan Boko Haram. Amma kuma yanzu sojojin gwamnati suka sake kwato yankunan daga hannun tsageru masu dauke da makamai.

'Yan gudun hijiran suna neman ganin an taimake su da kudaden wajen sake gina gidaje, da lamuran harkokin rayuwa na yau da kullum. Yayin da wasu kuma suna nuna tararrabi da zaman lafiyar da aka samu, inda suka nemi ganin an kara yawan jami'an tsaro da aka tura.

Sauti da bidiyo akan labarin