1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Rikicn Chadi ya dauki hankalin duniya

Zainab Mohammed Abubakar SB
May 7, 2021

Shugaban Emmanuel Macron na Faransa dai ya kasance shugaban Turai daya tilo da ya halarci jana'izar tsohon Shugaba Idriss Deby a Chadi a karshen watan Afrilu kana Jamus za ta mayar wa Najeriya kayan tarihi.

https://p.dw.com/p/3t7Cl
Drei Raubkunst-Bronzen aus dem Land Benin
Hoto: picture-alliance/dpa/D. Bockwoldt

Jaridar Der Tagesspiegel a labarinta mai taken "Najeriya ta yaba wa hukumomin Jamus" jaridar ta ce sanarwar ba zata da gwamnatin tarayyar ta yi na cewar, za ta mayar da mafi yawan kayan tarihin masarautar Benin sama da dubu daya da ke jibge a gidajen kallon kayan tarihi da ke fadin kasar, ya samu martanin murna da godiya a bangaren wannan kasa ta yankin yammacin Afirka.

A cewar Victor Ehikhamenor da ke zama memba a kwamitin amintattu da ke da alhakin  ganin an samo irin wadannan kayan tarihi, wannan gagarumin mataki ne wajen gyara rashin adalcin da Turawan mulkin mallaka suka yi. Kuma idan har an cimma nasarar mayar da wadannan kayayyaki na tarihi, ko shakka babu sauran kasashe zasu bi sahu.

Benin Bronzeskulptur
Hoto: picture-alliance/akg-images/W. Forman

Sojojin Ingila ne dai suka sace wadannan kayan tarihi daga fadar basaraken Benin, bayan kifar da masarautar wadanda aka kerasu da tagulla wasu ma sassakar itatuwa na mutum mutumi, wadanda aka kera tsakanin karni na 16 zuwa 18, kuma ake alfahari da su. An sayerwa kasashen Amurka da Turai inda yanzu kayan ke sassa daban daban na nahiyoyin, mafi yawansu a gidan ajiye kayan tarihi na Birtaniya da ke da sama da 900.

Yanzu kuma bari mu duba sharhin da jaridar Die Welt ta wallafa mai taken "Chadinmu na cikin mawuyacin hali". Ta cigab da cewar, shugabanni masu salon mulkin kama karya irinsu marigayi Idris Deby na samun goyon bayan kasashen yammaci na Turai koda wane irin mummuna abu suke aikatawa da sunan yaki da ta'addanci. Bayan mutuwar Deby a yanzu, wajibi ne Turai ta tambayi kanta, dangane da inda alkiblarta ta dosa na cimma muradunta.

Tschad l Beerdigung von Präsident Idriss Déby Itno | Präsident Macron
Hoto: Christophe P. Tesson/Epa/AP/picture alliance

Shugaban Faransa Emmanuel Macron dai ya kasance shugaban Turai daya tilo da ya halarci jana'izar Deby a Chadi a karshen watan Afrilu, inda ya zauna agefen dansa Mahamat Deby, janar na soji da ya gaji kujerar mahaifinshi da 'yan tawaye suka kashe a filin daga. Tuni dai aka soke kundin tsarin mulkin kasar da ke bai wa shugaban majalisar damar karbar ragamar mulki bayan mutuwar shugabanta.

Faransan dai na muradin zaman lafiya a kasar data mulka a baya, fiye da koken take hakkin dan adam da ma karancin sinadran demokradiyya da kungiyoyin farar hula da 'yan adawa ke yi. Da mutuwar Idriss Deby wanda Macron ya kira "aboki" Chadi ta yi asarar mutum mafi muhimmanci da take da shi, da ma yankin Sahel gaba daya, a yaki da 'yan ta'adda.

"Kyakkyawar fata kan alluran cutar zazzabin cizon sauro" da haka ne jaridar Süddeutsche Zeitung ta bude sharhinta kan nasarar allurar cutar Malariya data jima tana cin karenta babu babbaka a kasashe masu dumnin yawa musamman na Afirka.

Gabun - Malaria Test
Hoto: Universität Tübingen/Christoph Jäckle

Jaridar ta ce a karon farko an cimma nasarar gwajin allurar rigakafin cutar Malariya, da aka tabbatar da cewar tana bada kariyar wajen kashi 75. Duk da cewar ba a tabbatar da wannan nasarar ba, kasashen Afirka sun yi maraba da wannan yunkuri, tare da jaddada samar da kudi domin aiwatar da shi.

Kwararru a fannin kimiya daga jami'ar Oxford dake cikin tawagar da suka sarrafa allurar Astra-Zeneca ta COVID 19, tare da hadin gwiwar takwarorinsu na Afirka, suka sanar da yiwuwar samar da allurar ta Malariya da ka iya bada kariyar sama da kaso 75 kamar yadda hukumar kula da lafiya ta MDD ayyana.

An yi gwajin allurar a jikin yara da matasa kimanin 450 a kasar Burkina Faso.