Mayakan Siriya na zama hadari ga Jamus | Labarai | DW | 11.06.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Mayakan Siriya na zama hadari ga Jamus

Hukumar leken asirin Jamus ta bayyana Jamusawa sojin sa kai da suka fafata a yakin Siriya da suka dawo kasar a matsayin babbar barazana.

Hukumomin kare kundin tsarin mulkin tarayyar Jamus sun ayyana wadanda ke dawo kasar daga yakin Siriya a matsayin babbar barazana ga tsaron kasar ta Jamus. Shugaban hukumar Hans-Georg Maaßen ya ce harin da aka kai a birnin Brussels na kasar Belgium ya tabbatar da zargin da hukumar ta yi cewa sojojin sa kai Jamusawa da suka dawo daga yankunan da ake yaki a Siriya ka iya zama babban hadari. Ya ba da misali da mutumin da ya harbe mutane uku har lahira a gidan adana kayan tarihin Yahudawa da ke birnin Brussels a cikin watan Mayu, wanda ya yi yaki a bangaren 'yan tawayen Siriya. Maaßen ya ce tun bayan barkewar yakin Siriya shekaru uku da suka gabata, 'yan Islama 320 daga Jamus sun shiga Siriya, kuma yanzu haka kimanin 100 sun dawo kasar. Sai dai ya ce kawo yanzu hukumomin sa ba su samu wasu kwararan bayanai da zai ba su damar bibiyar wani yunkuri na kai wa kasar harin ta'addanci ba.

Mawallafi: Mohammad Nasiru Awal
Edita: Usman Shehu Usman