Mayakan Kurdawa sun kwace wani gari | Labarai | DW | 16.06.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Mayakan Kurdawa sun kwace wani gari

Mayakan Kurdawa na kasar Siriya sun kwace garin Tal Abyad daga hannun tsagerun kungiyar IS

Mayakan Kurdawa na kasar Siriya da suke fafatawa da tsagerun kungiyar IS masu neman kafa daular Islama, sun kwace garin Tal Abyad mai mahimmanci da ke kan iyakar Siriya da Turkiya.

Wannan nasara za ta taimaka wajen dakile daya daga cikin hanyoyin da tsagerun na kungiyar IS ke safarar kaya daga kasar Turkiya. Kungiyar saka ido kan kare hakkin dan Adam ta kasar Siriya ta ce an hallaka tsageru 40 yayin fatawar tare da taimakon jiragen saman yakin kasar Amirka.