1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kisan ma'aitakan sa kai a Burkina Faso

Binta Aliyu Zurmi
April 15, 2021

Akalla mutane 8 daga cikin ma'aikatan sa kai masu rajin kare kasar su da ake kira "Vounteers for the defence of motherland" ne suka rasa rayukansu a wani harin kwantan bauna da mayakan jihadi suka kai musu a daren jiya.

https://p.dw.com/p/3s2jM
Burkina Faso Nach den Anschlägen
Hoto: Getty Images/AFP/A. Ouoba

Harin ya auku ne a lokacin da ma'aikatan ke aikin tsaro na sinitiri a yanjkin arewacin kasar.

Maikatan sun bi sahun wasu barayi dabbobi ne da suka yi awon gaba da busashe a lokacin da 'yan bindigar suka hallakasu a Siguidi kusa da lardin Gorasdi

A shakarar 2019 ne aka kafa wannan kungiya ta VDP da zummar taimakawa jami'an soji yaki da mayakan da ke gwagwarmaya da makamai, amma suna fama da munanan hare-hare a lokuta da dama wanda tun daga shekara bara kawo yanzu aka kashe sama da mutum 200 daga cikinsu.

Ire-iren wadannan hare-haren a kan farafen hula da masu bada agaji na kara karuwa a koda yaushe wanda a 'yan kwanakin nan, Majalisar Dinkin Duniya ta sanar da kwashe ma'aikatanta daga shiyar arewa maso gabashin Najeriya bayan wani hari a offishinsu.