Mayakan Islama a Somalia sun janye daga bakin daga | Labarai | DW | 26.12.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Mayakan Islama a Somalia sun janye daga bakin daga

Jiragen saman yakin kasar Ethiopia sun sake kai farmaki akan mayakan Islama. Yanzu haka dai sojojin sa kai na ´yan Islama sun janye daga wurare da dama inda suka ja daga da farko. To amma sun bayyana haka da cewa ba tsoro ba ne illa sun ja da baya ne don su sake yin shiri. A na ta bangaren gwamnatin wucin gadin Somalia ta bayyana haka a matsayin wata nasara akan mayakan na kotunan Islama. Kungiyar tarayyar Afirka AU ta yi kira ga marikitan da su tsagaita wuta, amma a lokaci daya ta kare matakin sojin da Ethiopia ke dauka a rikicin na Somalia. Mukaddashin shugaban hukumar kungiyar AU Patrick Mazimhaka ya ce Ethiopia na da ´yancin kare kanta daga barazanar da ta ke fuskanta daga sojojin sa kan na ´yan Islama. Ita kuwa KTT gargadi ta yi game da bazuwar rikicin a yankin kahon Afirka gaba daya.