Mayakan IS sun halaka limami a Siriya | Labarai | DW | 08.01.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Mayakan IS sun halaka limami a Siriya

Masu fafutuka da bindiga na IS sun fille kan wani malamin addinin Islama a Syriya saboda a cewarsu ya yi kalaman batanci ga mahalicci Allah (SWT).

Da yammacin ranar Alhamis ne mayakan na IS suka sare kan wani limamin masallaci a garin Abu Khuyut a kusa da birnin Hasakeh a Arewa maso gabashin Siriya a cewar Kungiyar kare hakkin bil'Adama da ke sanya idanu kan rikicin kasar ta Siriya.

A cewar kungiyar mai sanya idanu da ke da sansani a Birtaniya uku daga cikin 'ya'yan malamin na daga cikin mayakan na kungiyar IS. Wannan kuma na zama karon farko da masu ikirarin jihadin sukan halaka wani malamin addini .