Mayaƙan IS sun rusa kushewu a Siriya | Labarai | DW | 23.06.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Mayaƙan IS sun rusa kushewu a Siriya

Masu yin jihadi na Ƙungiyar IS a Siriya sun ragargaza wasu kushewu guda biyu a garin Palmyra mai arzikin kayan tarihi.

Babban darakatan kula da kayan tarhi na Siriya Maamoun Abdel Karin ya ce a cikin kwanaki ukun da suka wuce masu tada ƙayar bayan sun rusa kushewar Mohammad Ben Ali, wanda ya fito daga iyalen Ali Ben Taleb tabashi ga Manzon Allah amince Allah da tsira su tabbata a kansa.

Kafin daga bisani sun tayar da nakiya a kushewar Nizar Abu Bahaeddine wani shehin mallamin kana waliyi wanda kushewarsa ta yi kusan shekaru 500.
Hakana kuma mayaƙan sun rusa wasu ƙaburburan jama'a a garin na Palimyra waɗanda aka gina,saboda abin da suka kira cewar ya saɓa wa addinin musulumci mayaƙan na Ƙungiyar IS su ci gari na Palmyra da yaƙi daga hannu dakarun gwamnatin Siriya wata guda da ya wuce.