Mayaƙan Iraƙi sun kashe wani ɗan jarida na Amirka | Labarai | DW | 20.08.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Mayaƙan Iraƙi sun kashe wani ɗan jarida na Amirka

'Yan bindigar da ke iƙirarin jihadi sun nuna wani bidiyo yadda suka hallaka mutumin bisa ɗaukar fansa na harin jiragen sama da Amirka ke kai musu a arewacin Iraƙi.

James Foley Journalist Reporter Libyen

Dan jarida, James Foley

Mayaƙan a cikin bidiyon sun nuna wasu mutane rufe da Fuskokinsu, lokacin da suka kashe James Foley, wanda ya ɓace a cikin ƙasar Siriya tun shekaru biyu da suka gabata.

Sun kuma nuna wani mutumin da suka sace, wanda suka ce shi ma, ransa ya ta'allaƙa ne kawai idan Amirka ta daina kai musu farmaki. A martanin da ta mayar fadar White House, ta ce jami'an leƙen asiri na binciken bidiyon don tabbatar da sahihancinsa. Amirka dai na kai farmakin soji kan mayaƙan a Iraƙi, musamman a Mosul, wanda tuni sojojin Iraƙi suka sake karɓe iko da yankin a farkon wannan mako.

Mawallafi: Usman Shehu Usman Edita: Abdourahamane Hassane